Wata babbar Kotun tarayya karkashin Mai Sharia Justice Taiwo Taiwo da ke zamanta a Abuja, ta ayyana Yan Bindiga a matsayin Yan Ta’adda.
Alkalin ya bayar da odan ex parte bayan Gwamnatin tarayya ta gabatar da bukatar haka a gaban Kotun.
Babban jami'i mai gabatar da kara na tarayya a ma'aikatar Sharia na kasa, (DPP) Mohammed Abubakar ne ya gabatar da takardun karar amadadin Gwamnatin tarayya, wanda a ciki Gwamnati ta bukaci Kotu ta ayyana Yan bindigan daji, Kungiyoyin masu aikata miyagun ayyuka a matsayin Yan ta'adda.
A cikin Takardun da aka gabatar a gaban Kotu, wasu Takardun da ke da alaka da harkokin tsaro sun tabbatar da cewa Yan bindigan ne ke da alhakin kashe-kashen bayin Allah, fyade, sace-sacen mutane da sauran ayyukan keta mutunci da haddin bil' adama a yankin arewa maso gabas da arewa maso tsakiyar Najeriya.
Rubuta ra ayin ka