Kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a Kofar Kudu a jihar Kano ta sake hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara beli bayan watanni da tsareshi, rahoton BBC Hausa.
Muhammad A Mika’il, wanda ke wakiltan Malam AbdulJabbar a kotu ya sake gabatar da bukatar gaban mai Shar'ia Ibrahim Sarki Yola a zaman kotun da aka yi ranar Alhamis, 25 ga Nuwamba, 2021.
Kotu tace za'a yi zama na gaba ranar 9 ga watan Disamba, 2021.
BBC ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Kano ta bi umurnin da kotu tayi na cewa a baiwa Malam AbdulJabbar kudi N20,000 don ya sayi litattafai kuma a kawo masa littafin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim.
Kotun Shari'a ta sake hana beli Shehin Malami
A cigaba da garkame Abdul-Jabbar, Kotun Shari'a ta sake hana beli Shehin Malami Hoto: BBC Hausa Source: UGC
Legit
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI