Shahrarren Malaman addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa dillalan muggan kwayoyi da masu fataucin makamai ne suka mayar da Fulani Makiyaya yan bindiga.
Fulani Makiyaya a shekarun nan sun addabi al'ummar Najeriya, musamman yankin Arewa maso yamma. Sheikh Gumi ya kasance mutum daya tilo da samu ganawa da yan bindiga domin yi musu wa'azi su daina garkuwa da mutane. Malamin a jawabin da yayi a taron zaman lafiya da cibiyar mutunta rayukan mutum ta shirya a Arewa House dake jihar Kaduna ranar Alhamis, rahoton Tribune.
Gumi ya ce hanya daya tilo da za'a bi domin kawo karshen barandanci shine raba alakar dake tsakanin dillalan kwayoyi da makamai da kuma Makiyaya.
Ya ce "Idan mugayen mutane sun ja hankalinsu, yan kwaya, masu fataucin bindiga, kada mu bari a yi amfani da su. Wajibi ne mu dawo da su cikin al'umma, abinda muke bukata kenan. Su ma ya kamata a mutuntasu, kuma a basu dukkan hakkokinsu na dan Adam."
Legit Hausa
Rubuta ra ayin ka