Shin ko teɓa na hana haihuwa?


Likitoci sun ce kibar da ta wuce kima nau'i biyu ce, ta waje da kuma ta cikin mutum. Sai dai ta cikin ta fi hadari, domin ta kan shafi al'adar mace.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce an fi samun mutane masu teba, a kan wadanda kibarsu ta wuce kima, a kowane yanki na duniya.

Amma ban da yankin Kudu da hamadar Sahara Afrika da kuma yankin Asia.

A cewar hukumar wannan matsalar a baya ta fi kamari ne a kasashen da suka ci gaba.

Sai dai a yanzu matsalar teba na karuwa a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga, musamman a birane.

WHO ta bayyana cewa matukar kiba ko teba da kan shafi kiwon lafiya, abu ne da ya kai matakin annoba a duniya.

Inda kimanin mutane fiye da miliyan hudu ke mutuwa duk shekara, a dalilin hakan.

Wasu na baya da za ku so

Alkaluman hukumar sun nuna cewa daga shekarar 1975 zuwa shekarar 2016, an samu yawaitar yara masu shekara biyar zuwa shekara 19, da ke fama da teba fiye da ninki hudu.

Wato daga kashi hudu cikin dari zuwa kashi 18 cikin dari, a cikin sama da shekara arba'in, a fadin duniya.

A shekarar 2019 kacal, an samu yara 'yan kasa da shekara biyar, miliyan 38 da dubu dari uku, wadanda ko dai kibarsu ta wuce kima ko kuma suna da matukar teba. In ji hukumar.

Hukumar ta kara da cewa ta bangaren manya kuma an samu kashi 39 cikin dari na wadanda kibarsu ta yi yawa sosai, yayin da masu teba sosai kuma suka kai kashi 13 cikin dari, a shekarar ta 2016.

Alkaluman da ke nufin a shekarar an samu manya biliyan daya da miliyan dari tara na da kibarsu ta wuce kima, yayin da a cikin wannan jimilla kuma yawan masu matukar teba ya kai miliyan 650.

Haka kuma mafiya yawan yaran da ke fama da teba an fi samunsu ne a kasashe masu tasowa.

Inda ake samun karuwarsu har ta kai sun haura na kasashen da suka ci gaba da kashi 30 cikin dari.

To domin jin cikakken bayani kan yadda matsalar teba ke shafar mata masu neman haihuwa da masu ciki, sai ku saurari hirar da Habiba Adamu ta yi da Dakta Mairo Mandara.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN