Yadda ‘Yan Bindiga Suke Kwasar Kashinsu A Hannunmu – Shalkwatar Tsaro


Shalkwatar tsaro ta bayyana cewa, sakamakon yaki da masu tayar da kayar baya da ‘yan bindiya da take yi, ta samu nasarar kashe ‘yan bindiga guda 436 da mambobin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP a fadin kasar nan cikin mako uku. Haka kuma takarun sojin sun damke ‘yan bindiga 105 da masu garkuwa da mutane da kuma masu bayar da bayanin sirri a yankunan Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso Yammacin kasar nan.


Mukaddashin Daraktar Yada Labarai na Shalkwatar Tsaro, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai da a garin Abuja. Ya bayyana cewa sakamakon samamen da dakarun soji suka gudanar a tsakanin ranar 2 ga watan Satumbar zuwa 30, sun sami nasarar kwato makamai masu yawan gaske da albarusai guda 12,250 da nakiyoyi da kuma sauran kayayyaki.


Onyeuko ya kara da cewa a tsakanin lokacin wannan kiddigar, dakarun sojin sun tsananta kai hare-hare kan ‘yan bindigar da ke yankin Arewa maso Yamma ta sama da kuma ta kasa wanda ya yi sanadiyyar babbake maboyarsu a sassa daban-daban. Ya ce hare-haren ya hana su sakat wanda ya janjo suka kasa safarar bindigogi da albarusai da sauran miyagun makamai daga wannan yanki zuwa wancan.


Rundunar OPERATION HADIN KAI


Rundunar Operation Hadin Kai ta samu nasarar kama makayan Boko Haram da ISWAP da ‘yan ta’adda guda 43 wadanda suka hada da masu taimaka musu da masu sararar makai a wasu hare-hare da dama da ta gudanar. Haka kuma ta samu nasarar kwato jimillar makamai guda 121 wadanda suka hada da bindigogin kirar SMG, HK21, AK-47 da kirar gida tare da albarusai guda 3,372 da harsasai na musamma na NATO da kananan bindigogi kirar gida da gurneti da bama-bamai 12,250 da buhunan taki da dabbobin da aka sace 178. Bugu da kari, ta samu nasarar kama ‘yan ta’adda jimillar 2,783 da iyalansu da suka mika wuya lokacin wannan kididdigar.


Rundunar OPERATION HADARIN DAJI


Rundunar Operation Hadarin Daji ta bayyana cewa a lokacin wannan kididdigar, dakarunta ta samu amsa waya a kan ayyukan ‘yan ta’adda a sassa daban-daban na jihohin Zamfara, Sakkwato da kuma Katsina. Wadannan sun hada da farmakin da ‘yan bindiga suka kai a kauyan Gidan Kwaru da ke cikin karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da yankin Kaiga da kauyen Tafoki a karamar hukumar Funtua ta Jihar Katsina State.


Sauran sun hada da farmakin ‘yan bindiga na garin Burkusuma da kauye Makuwana a karamar hukumar Sabon-Birni ta Jihar Sakkwato da kuma na Garin Sabuwa lokacin da ‘yan bindiga suka toshe hanyar Gimi zuwa Gora a Jihar Katsina. Nan take dakarun sojin suka dauki mataki wanda suka ci karfin ‘yan bindigar, inda suka samu nasarar cafke wasu da masu kai musu bayanai da kuma masu taimaka musu, yayin da wasu suka gudu. Haka kuma an samu nasarar kwato bindigogi da makamai da sauran abubuwa masu fashewa.


Hakazalika, dakarun sojin sun samu nasarar damke ‘yan bindiga da masu safarar makamai da masu ba su bayanai a kauyukan Kofar Fada da ke karamar hukumar Kankara da Shabba da ke karamar hukumar Jibia da Kaigageneral tare da Ummandau da Gammu, dukkan su a cikin jihar.


Har ila yau, dakarun sojin sun yi arangama da ‘yan bindiga a yankunan Falaliya, Yan Duwatsu, Kunkare, Jangeme, Mazarko da Kasala da suke cikin karamar hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara da kauyan Yarmariya da ke karamar hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano tare da shafe damar ‘yan bindigar. A lokacin wannan artabu, sojoji sun sami nasarar kama ‘yan bindiga guda 240 da bindigogi 125 wadanda suka hada da kirar AK-47 da bindogin toka da harsasai na musamman na NATO 1,166 da shanu 1,304 da babura 54 da sauran kayayyaki. Haka kuma sun damke masu kai wa ‘yan bindiga bayanai guda 47 a wannan lokaci.


A wani lamari makamancin wannan, rundunar sojojin sama sun babbake maboyan ‘yan bindiga a yankuna daban-daban wadanda suka hada da dazukan Magami da Dansadau da ke Jihar Zamfara. Haka kuma jirgin yakin rundunar sojan sama ya yi kuskuran kai hari kan fararen hula lokacin da yake farmakan ‘yan bindiga a tsakanin ranar 22 zuwa 26 na watan Satumbar 2021. Rundunar sojojin saman Nijeriya sun yi artabu da ‘yan bidiga a kauyukan Danmusa, Safana, Dutsinma, Gonar, Sani, Jikan, dazukan Malam,Yantumaki, Lelet da kuma Yantumaki  da ke kan hanyar Maidabino ta Jihar Katsina. A lokacin wannan artabu, an samu nasarar kashe ‘yan bindiga 53, yayin da sauran suka gudu da raunikan harbin bindiga a jikinsu da kuma kwato kayayyaki da suka amfani da su.


Rundunar OPERATION SAFE HABEN


Rundunar OPERATION SAFE HABEN ta bayyana cewa dakarunta sun kai samame masu yawa a mafakar ‘yan ta’adda. Dakarun sun sami kiran wayar salula a ranar 4 ga watan Satumbar 2021, inda suka kama dilolin mayagun kwayoyi guda biyu tare da hodar Iblis wacce kudinta ya kai na naira miliyan tara da dari shida a kan hanyar Ganawuri zuwa Manchok. Haka kuma a wannan rana sun sami nasarar raba rikici a tsakanin namoma da Funali Makiyaya a kauyen Jebbu Miango da ke karamar hukumar Bassa a Jihar Filato. An dai kama Makiyaya guda biyu a wannan lokaci. A ranar 6 ga watan Satumba, dakarun sojin sun yi nasarar cafke ‘yan bindiga 11 wadanda suka kai hari a Angwan Thabo.

Rahotun Jaridar leadership

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN