Mawallafin shafin labarai na Sahara Reporters Omoyele Sowere ya sha dan karen duka a hannun yan daba a harabar babban Kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba.
Sowere yana tsaye tare da jami'an tsaro yana yi masu bayani a mashigar babban Kotun domin ya halarci zaman Kotu kan shari'ar Nnamdi Kanu. Kwatsam sai wasu yan daba kimanin su 20 suka bayyana suka yi masa duka nan take, kuma suka bar wajen a cewar Labarin Jaridar The Nation.
Lamari da ya jawo bacin rai ga wasu jama'a da ke wajen, duba da yadda aka bari har yan daban suka kai wajen Sowere kuma suka yi masa duka.