Kada a baiwa masu tsatsauran ra'ayi damar shugabantar Najeriya, matukar ana son a kawo karshen rashin tsaron da ya addabi kasar, cewar Sarkin Musulmi

Daga Comr Abba Sani Pantami


Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci hukumomin tsaron kasar tare da shugabannin siyasa da su tashi tsaye wajen ganin sun murkushe duk wasu masu bukatar jefa Najeriya cikin tashin hankali ta hanyar wa’azin da suke gudanarwa.

Sarkin Musulmi ya bayyana cewar mutane da dama na amfani da Addini wajen mummunar fassara domin biyan bukatar kan su, saboda babu wanda ke tankwasa su, musamman daga cikin manyan addinan kasar guda biyu.

Sarkin Musulmi ya bayyana wannan matsalar a matsayin babbar kalubalen da ya addabe su, saboda haka ya dace a rungumi shirin bayar da ilimi domin kawar da matsalar tsatsauran ra’ayi a cikin al’umma.

Sarkin Musulmi ya bukaci hukumomin Najeriya da su dauki duk matakin da ya dace wajen hana masu tsatsauran ra’ayi karbe ragamar tafiyar da kasar ta hanyar amfani da addini da kuma matakan tsaro.

Daga karshe Sarkin Musulmi ya bayyana matsalar rashin amfani da shawarwarin masana wajen shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya a matsayin babban kuskuren da ya sanya Najeriya a cikin yanayin da ta samu kan ta a yau.

Shugaban sojin kasa na Najeriya Lafatanar Janar Faruk Yahya ya bayyana cewar ana iya shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar muddin kowa ya bada gudumawar da ake bukata.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN