Da duminsa: An sako Yara 30 daga daliban makarantar sakandare na FGC Birnin Yauri da yan bindiga suka sace


An sako dalibai 30 daga cikin daliban makarantar sakandare FGC Birnin Yauri da yan bindiga suka sace watanni hudu da suka gabata.

Wadanda aka sako sun hada da dalibai 27, da suka hada da maza 25 da mata 2. Da kuma malamai maza guda 2 da Malama mace guda daya. 

Wata Takarda da mai taimakawa wa Gwamnan jihar Kebbi kan harkar labarai Yahaya Sarki ya fitar ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba ya ce:

"Dalibai 30 daga cikin dalibai na makarantar Sakandare na FGC Birnin Yauri da yan bindiga suka dauke sun iso Birnin kebbi bayan an sako su. 

Ana ci gaba da kokarin ganin an sako sauran yaran.

Za a tantance lafiyarsu yayin da ake kokarin sada su da iyalinsu" ya ce.

Takardar ta yi godiya ga jama'a da suka taimaka aka sako daliban. Yayin da sanarwar ta yi jinjina ga shugaba Muhammadu Buhari kan nassara da aka samu. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN