Yansandan jihar Adamawa sun ceto Hauwa Umaru da diyarta bayan yan bindiga sun yi awon gaba da ita da diyar. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.
Hauwa tana zaman takaba ne lokacin da yan bindigan suka sace ta tare da diyarta.
Kakakin hukumar yansandan jihar Adamawa DSP Suleiman Ngoroje, ya ce yan bindigan sun saki Hauwa da diyarta ne suka tsere bayan yansanda da yan banga sun bi su cikin daji.
Ya ce Hauwa da diyarta suna samun kulawan Likita domin tabbatar da lafiyarsu.
Rubuta ra ayin ka