Type Here to Get Search Results !

Kudan zuma sun lullube kwarto yana tsakar lalata da matar aure a cikin daji suka yi ta harbinsa


Kudan zuma sun farmaki wani mutum yayin da yake tsakar aikata lalata da wata matar aure a kauyen Kwaramba da ke garin Gokwe a kasar Zimbabwe. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Mutumin mai suna Jethro Maimba yana tsakar aikata lalata da matar aure mai suna Lizzie Maphosa a cikin daji, sai kudan zuma suka lullube shi suka yi ta harbinsa.

Mun samo cewa mijin Maphosa ya sha jan kunnenta kan zargin da ake mata na mumunan hulda da Jethro Maimba. Daga bisani mijin mai suna Joseph Musariri ya tsine masu kuma ya yi masu mugun baki.

Kazalika mun samo cewa kudan zuman sun daina bin Maimba ne bayan ya nemi gafarar mijin matar mai suna Musariri

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies