Yadda miji zai tafiyar da matarsa idan tana cikin fushi


A mafi yawan lokuta namiji zai wayi gari ya ga matarsa na fushi da ciccin magani tana ta basarwa. Juyin duniyar nan ya bi ta don ya san me ke damunta ko laifin da ya yi mata amma sai abin ya ci tura.

Wani ma sai ya fara tsarguwa ya fara tambayar kansa 'to ko dai ta ɗauki wayata ta ga wani abu ne? Sai kuma ya tuna au to yaushe rabon ma da na yi chatin da wata.'

Can kuma kamar mai sauka daga bori sai ya ga ta dawo kamar da ta washe an ci gaba da harkoki.

Wannan irin fushi kan ɗaga wa mafi yawan maza hankali duk su kasa sukuni.

A Turance ana kiran wannan yanayi da Mood Swings, wato sassauyawar ɗabi'a. Amma mene ne yake jawo shi ne?

Masana halayyar ɗan adam da likitoci sun ce yawanci wannan ɗabi'a ta fi shafar mata sakamakon sauyawar sinadaran halittarta wato hormones.

A irin wannan lokaci da sinadaran ke sauyawa sai mace ta dinga fushi ba gaira ba dalili, ko ta ji ta tsani ji da ganin kowa a kusa da ita. Wata ma har ta dinga koke-koke ba duka ba zagi.

Wata ta fi shiga irin wannan yanayi da safe, wata kuma da rana, wata sai yamma. Sannan abin kan ɗauki lokaci a tare da wasu matan, wasu kuma nan da nan abin ya wuce.

Mafi yawan mata sun fi shiga wannan yanayi idan suna da ciki ko idan suna haila.

A hirar da na yi da mata da yawa, sun shaida min cewa suna yawan samun kansu a irin wannan yanayi kuma ba taree da an musu komai ba.

Wannan layi ne
Wasu sun gaya min cewa sun yi bincike sun gano dalilin da ya sa suke da wannan ɗabi'a, yayin da wasu kuma suka ce ba su taɓa sanin dalili ba.

Ni ma a kan kaina na kan shiga wannan yanayi sau da dama, har ma a lokutan da nake cikin nishaɗi maigidana kan ce min 'wallahi ba na so na gan ki a wannan yanayi, ɗaga min hankali kike yi, sai na ga kamar ni na yi miki wani laifi.'

Wasu lokutan kuma matuƙar gajiya kan sa mace ta shiga yanayi na mood swings.

Duk da cewa ba ni da wata ƙididdiga, amma ina hasashen cewa wataƙila aurarraki da yawa sun sha mutuwa a cikin al'ummar sakamakon irin wannan tarnaƙi.

Don idan ba a yi sa'a ba mace tana wannan ɗacin ran, wani namiji ya bi ta ta gaya masa matsalar amma ta ƙi rikici na iya kaurewa a tsakaninsu daga nan idan ƙaddara ta gifto sai a yi saki.

Wataƙila sakin ma ya kasance mummunan wato saki uku, wanda sai daga baya idan hankula sun nutsu sai a shiga da-na-sani kuma.

To wane mataki ya kamata maza su bi?

Malam Ishaq Guibi wani malami ne a Kwalejin Fasaha ta Kaduna a sashen nazarin harsuna, kuma yana da mata uku, ya shaida min cewa a irin waɗannan lokuta da mata kan samu kansu cikin mood swing lallai akwai buƙatar namiji ya yi taka tsantsan.

"A irin wannan lokaci dole ne ka zama mai yin nesa-nesa da ita. Ka ma fita daga gidan idan da hali. Kar ka matsa lallai sai ka ji me ke damunta.

"Amma idan za ka koma gida ka nemi wata ƴar kyauta da za ta faranta mata rai," yin irin waɗannan na rage kaifin samun matsala sakamakon yanayin da take cikin," a cewar Malam Ishaq.

Sannan wani abu da miji zai iya yi a wannan lokaci shi ne aika mata da saƙonnin nuna ƙauna ta wayarta. Kar kuma ka ce za ka biye ta kai ma ka hau dokin fushin, wannan ba zai ƙara wa matsalar komai ba sai rura wutarta.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN