Mene ne zai sauya idan aka ayyana 'yan fashin daji a matsayin 'yan ta'adda?


Mafi yawan ayyukan 'yan fashi na daji ko na gida sun fi kama da na 'yan ta'adda amma duk da haka ba 'yan ta'adda ba ne a yaren gwamnati. Kuma duk da kiraye-kirayen da masu faÉ—a-a-ji ke yi gwamnatin Shugaba Buhari ta ki amincewa da bukatar ayyana su matsayin 'yan ta'adda.

A wani hari da 'yan fashin dajin suka kai garin Goronyo na Jihar Sokoto kasa da mako biyu da suka wuce sai da suka kashe mutum 43 ana tsaka da cin kasuwar mako ta garin.

Wannan na faruwa ne ƙari a kan ɗaruruwan 'yan makaranta da suka sace da kuma yi wa mata fyade a garuruwa daba-daban.

Amma mene ne zai sauya a yaƙi da 'yan fashin idan aka ayyana su 'yan ta'adda?

Mece ce ma'anar ta'addanci?

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram
Bayanan hoto, Najeriya da sauran ƙasashen duniya na kiran ƙungiyar Boko Haram da masu alaƙa da ita a matsayin 'yan ta'adda
Duk da cewa babu wata tartibiyar ma'ana da ƙwararru suka haɗu a kanta da suka bai wa ta'addanci, Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a ƙudiri mai lamba 49/60 cewa za a iya fayyace aikin ta'addanci kamar haka:

"Wani aiki da aka aikata da nufin saka jama'a cikin tashin hankali, ko kuma wani rukunin mutane ko wasu mutane da manufar siyasa ba tare dawani dalili ba, ko da kuwa mece ce manufarsu a siyasance, ko aƙida, ko tunani, ko launi, ko ƙabila, ko addini ko kuma duk wata hanya da za a bi wajen kafa hujjar yin hakan."

A Najeriya, Dokar Ta'addanci ta 2011 ta tanadi hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin aikata ko taimaka wa wanda ya aikata ta'addanci. Sai dai an yi wa dokar kwaskwarima a 2013 inda aka mayar da hukuncin zuwa ɗaurin ra-da-rai ga wanda ya aikata da kuma hukuncin ɗaurin shekara 20 mafi ƙaranci ga wanda ya taimaka.

Sai dai dokar ba ta fayyace haƙiƙanin ma'anar ta'addanci ba.

Idan ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda, gwamnatin Najeriya ka iya kafa kotuna na musamman domin yi wa 'yan fashin daji shari'a da zummar yanke musu hukunci cikin sauri.

Kazalika, za ta iya matsa wa ƙasashe maƙota wajen taso ƙeyar duk wanda ta zarga da shiga ayyukan fashin daji idan ya tsallaka kan iyaka. Sai dai ba lallai ne ƙasashen su kalle su a matsayin 'yan ta'adda ba.

Kiran bayan-bayan nan da masu faÉ—a-a-ji suka yi wa gwamnatin Najeriya kan ta ayyana 'yan fashin matsayin 'yan ta'adda ya fito ne daga bakin gamayyar majalisun jihohi 36.

Majalisar Dattawan Najeriya da ta wakilai duka sun nemi Shugaba Buhari ya yi hakan.

Bayan taron da ta gudanar a Jihar Katsina ranar 23 ga watan Oktoba, gamayyar State Legislators of Nigeria ta buƙaci gwamnatin Abuja ta sauya dabara wajen yaƙin da 'yan fashin.

Tun farko, shi ma Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya nemi gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin tsaro a Najeriya da zummar kawo ƙarshen kashe-kashen.

Kwana uku kafin haka, Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya ce jiharsa na kan gaba wajen neman a ayyana su 'yan ta'adda domin sauwake yaƙin da ake yi da su.

Wasu 'yan siyasa a kudu da ma arewacin Najeriya na sukar Buhari kan ayyana ƙungiyar masu fafutikar kafa ƙasar Biafra 'yan ta'adda amma ya gaza yin hakan kan 'yan fashin daji.

Sai dai shugaban ya taɓa bai wa jami'an tsaro umarnin cewa "a harbi duk wanda aka gani da bindigar AK-47" da zummar daƙile ayyukan 'yan fashin.

Mahukunta a Najeriya da suka haɗa da gwamnoni da masana harkar tsaro na cewa ayyana 'yan fashin daji a matsayin 'yan ta'adda zai sauya akalar yaƙi da su.

Da yake magana jim kaɗan bayan miƙa masa rahoto kan matsalar tsaro a jihar Kaduna, Gwamna El-Rufai ya ce babu wata hanyar yaƙi da 'yan fashin daji illa "yi musu ruwan wuta a lokaci guda", abin da ya sa yake son a ayyana su 'yan ta'adda kenan.

"Mun rubuta wasiƙu ga gwamnatin tarayya tun 2017 muna neman a yi hakan saboda ayyana su ne kaɗai zai bai wa sojoji damar karkashe waɗannan 'yan fashin ba tare da wani abu ya biyo baya ba daga ƙasashen duniya."

Shi ma wani masanin harkar tsaro, Manjo Muhammadu Bashir Galma (mai ritaya), yana ganin ayyana su a matsayin 'yan ta'adda shi ne ya fi dacewa.

"Dukkan ayyukan da 'yan ta'adda ke yi su ma ('yan fashin daji) sun aikata shi," in ji shi.

"Duk wanda zai shiga wuraren ibada, kamar masallaci da coci da kasuwa, ya baza mutane, ko kuma 'yan makaranta suna barci a kwashe su a shigar da su daji a wulakanta su, wannan abin da suke yi shi ake kira ta'addanci."

A cewarsa: "Duk wanda ya aikata wa wani ta'addanci sau biyu ko sau uku kuma bai tuba ba É—an ta'adda ya kamata a kira shi."

'Babu tabbas ko hakan zai yi tasiri'

A wajen masanin tsaro Kaftin Sadik Garba (mai ritaya), babu wani tabbacin nasara ko sauyi game da ayyana 'yan fashin a matsayin 'yan ta'adda "ganin cewa a yanzu ma jami'an tsaro na kashe su".

Sai dai yana ganin idan aka yi hakan to gwamnati ta amsa kiran da 'yan Najeriya suka yi mata na aiwatar da abin da suka nema.

"A matsayina na masanin tsaro, zan ce idan wani alheri ake son samu to sai dai a ce gwamnati ta samu (alheri) kan cewa ta amsa kukan mutane, an yi musu yadda suke so.

"Amma a É“angaren tsaro, babu wani tabbas kan ko hakan zai yi wani tasiri saboda ko yanzu ma da ba a kira su 'yan ta'adda ba jami'an tsaro na kai musu hari ne da duk abin da suke da shi amma har yanzu ba a ci nasara ba."

Ya ƙara da cewa hatta jiragen yaƙi da Amurka ta sayar wa Najeriya na Super Tucano sai da ta saka sharuɗɗa kuma a lokacin babu 'yan fashin daji.

Jihohin da 'yan fashin daji suka fi addaba:

Daga cikin alfanun da wasu ke faÉ—a shi ne ayyana su a matsayin 'yan ta'adda zai bai wa sojoji damar bin su har sansanoninsu tare da kashe su gabagaÉ—i duk da cewa suna zaune da iyalansu a dazuka.

Sai dai Manjo Bashir Galma ya ce hakan ba ya nufin sojoji ba za su bi doka ba.

"Sojoji fa ba mahaukata ba ne, ba yadda za a yi soja ya je ya buÉ—e wa mutane wuta a daji kawai saboda suna tare da 'yan fashi, sai dai fa idan suna taimaka wa 'yan fashin ne.

"Ko da an ayyana su 'yan ta'adda har yanzu dokokin aiki na nan kuma su sojojin sun sani an koya musu, za su bi su."

'Ƴan ta'adda' a Najeriya
Abu sanannne cewa gwamnatin Najeriya ta sha ayyana wasu ƙungiyoyi a matsayin na 'yan ta'adda kafin wannan lokaci.

A watan Satumban 2017 ne wata Babbar Kotun Tarayya ta haramta ayyukan ƙungiyar Indigenous People Of Biafra (IPOB), wadda ke fafutikar kafa ƙasar Biafra, sannan ta ayyana ta matsayin ta ta'addanci.

Kazalika, gwamnati ta haramta ayyukan ƙungiyar 'yan Shi'a mabiya Ibrahim El-Zakzaky, Islamic Movement in Nigeria (IMN) a 2019.

Idan ba a manta ba kuma, fiye da shekara 10 kenan da gwamnatin Najeriya ta fara kallon ƙungiyar Boko Haram a matsayin ta 'yan ta'adda kuma yaƙin da gwamnati ke yi da ƙungiyar ya yi sanadiyyar kashe mutum fiye da 200,000, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Duk sanda aka samu irin wannan haramci kan wata ƙungiya hakan na nufin duk wanda aka kama yana bayyana kansa a matsayin mambanta gwamnati za ta iya gurfanar da shi a gaban kotu.

Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya sha neman a karkashe 'yan fashin daji lokaci guda

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na Jihar Kaduna ya shawarci gwamnatin Najeriya ta ɗauki matasa 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma aikin bayar da tsaro don yaƙar 'yan fashin daji masu garkuwa da mutane.

Da yake magana jim kaɗan bayan miƙa masa rahoto kan matsalar tsaro a jihar ranar Laraba, El-Rufai ya ce babu wata hanyar yaƙi da 'yan fashin daji illa "yi musu ruwan wuta a lokaci guda", abin da ya sa yake son a ɗauki matasa 774,000 aikin.

"Ina kira ga jihohi 36 da su ɓullo da wani shirin gaggawa na ɗaukar mutane aiki a rundunonin tsaro. Gwamnati ka iya sauya halin da ake ciki idan ta ɗauki matasa 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma a faɗin ƙasa.

"Hakan zai zama gagarumin adadi na dakaru a fagen daga tun bayan yaƙin basasa (na Biafra). Adadin sabbin dakaru 774,000 a filin yaƙi zai kasance babbar hanyar gamawa da miyagu da kuma samar da aikin yi."

Sabon rahoton da aka gabatar wa El-Rufai a yau ya nuna cewa mutum 343 aka kashe a Kaduna daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021 sakamakon ayyukan 'yan fashi da kuma rikicin ƙabilanci a jihar.

Haka nan, 'yan fashin dajin sun sace mutum 830 cikin wata ukun da rahoton ya bayar da bayanai a kai tare da raunata 210.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN