Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a game da rade-radin da ake yi na cewa yana shirin barin PDP. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har gobe yana nan a jam’iyyar PDP. Kwankwaso ya yi karin-haske da aka yi hira da shi a gidan talabijin Arise.
Shugaban darikar siyasar Kwankwasiyyan ya yi wannan martani ne yayin da aka jefa masa tambaya kai-tsaye da ake hira da shi a game da makomarsa.
“Har yanzu ni ‘dan jam’iyyar PDP ne.” - Kwankwaso Tsohon Ministan yace zai yi zamansa a jam’iyyar hamayya ta PDP, ya hada-kai da sauran abokan aikinsa wajen ganin an shawo kan rikicin cikin gidansu.
Rabiu Musa Kwankwaso ya karyata rade-radin cewa akwai yiwuwar ya koma jam’iyyar APC mai mulki Tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya bayyana cewa har gobe yana nan jam’iyyar hamayya ta PDP
Da aka yi hira da Kwankwaso a gidan talabijin dazu, yace zai cigaba da bada gudumuwa a jam’iyya
Legit Hausa
Rubuta ra ayin ka