Tap di jan: Wata budurwa ta fito tallar kanta a titi tana neman mijin aure


Wata kyakkyawar budurwa ta cire kunya ta fito neman mijin aure kan titi ɗauke da allon rubutu a yankin Buza da ke birnin Daris Salaam na kasar Tanzaniya, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Hakanan kuma budurwar ta bayyana cewa yawan shekarun namiji bai dame ta ba, bukatarta shine cika burinta na yin aure.

A wani hoton bidiyo da ya watsu, budurwar ta fito kan titi ɗauke da allo, wanda ke ɗauke da rubutun, "Ina neman mijin aure da ke tsakanin shekara 20 zuwa 70.”

Ni budurwace har yanzun

Budurwar ta bayyana cewa ta ɗauki nauyin al'amuran bikin auren ta, kama daga sadaki da sauransu, kuma a cewarta har yanzun ita budurwace, ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba.

Tace:

"Na ɗauki nauyin biyan sadaki, kuma tuni na tanaji zoben aure na, zan siya wa angon kayan da zai saka ranar biki, fatana in samu miji mai tsoron Allah."

Ko meyasa ta fito kan titi neman miji?

A cewarta, tana tsoron lokaci ya ƙure ba ta yi aure ba, don haka ya zama tilas a kanta ta ɗauki matakin da ya dace don kaucewa matsala.

"Kullum kara yawan shekaru nake ina ƙara tsufa, kuma ina bukatar namiji a tare da ni. Ina da yaƙinin cewa ban karya doka ba, ni na yanke wa kaina shawarar daukar wannan matakin."

Ina da kuɗi kuma zan ɗauki nauyin komai

Matar ta ƙara jaddada cewa ita mai kuɗi ce, a don haka babu wata matsala da ta shafi kuɗi matukar ta samu mijin da zai neme ta da aure.

A cewarta, ba wannan ne farkon da ta fito neman mijin aure ba, ta yi a baya, kuma zata cigaba da yin haka har sai ta cimma burinta.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN