Kotu ta rushe shugabannin kananan hukumomi da gwamna ya naɗa a wata jihar arewa


Babbar kotun jihar Kwara ta rushe kwamitin rikon kwarya da gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya naɗa domin su jagoranci kananan hukumomi 16 dake jihar.

Premium times ta ruwaito cewa gwamna AbdulRazaq ya naɗa shugabannin riko a ƙananan hukumomin jihar bayan dakatar da zababbu.

Amma a ranar Jumu'a, Mai shari'a Hassan Gegele, na babbar kotun jihar dake zama a Ilorin, ya bayyana matakin da gwamnan ya ɗauka da, "cin mutuncin mulki."

Gegele ya yi hukunci ne kan ƙarar da wata ƙungiyar al'umma ta shigar a gabansa, tana ƙalubalantar naɗa kwamitin riko da gwamnan jihar ya yi.

Shin gwamnatin Kwara ta amince da hukuncin?

Da yake martani kan hukuncin kotun, Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a, Salman Jawondo yace gwamnati zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Tribune ta rahoto Jawondo yace:

"Muna tabbatar da cewa shari'a kan wannan lamarin ba ta kare ba, domin zamu ɗaukaka ƙara zuwa kotun Allah ya isa."

PDP ta ji daɗin wannan hukuncin

Da take bayyana ra'ayinta kan hukuncin, babbar jam'iyyar hamayya PDP ta yaba da hukuncin kotun.

A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar PDP reshen jihar, Tunde Ashaolu, fitar ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke da, "Cigaba mai kyau."

Hakazalika PDP ta yaba wa ƙungiyar ENetSuD bisa namijin kokarinta wajen yaƙi da karya doka da kuma neman adalci.

Sanarwar tace:

"Hukuncin kotun bai zo mana da mamaki ba, domin ya zo dai-dai da matsayar mu cewa gwamna ba shi da ƙarfin sallamar zaɓaɓɓun ciyamomi."

"Hukuncin da kotu ta yanke yau nasara ce ga mulkin demokaradiyya da kuma al'ummar jihar Kwara, waɗanda ke neman a musu adalci."

A wani labarin kuma Gwamna Umahi ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindigan da suke tada yamutsi a jiharsa

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa ba zai sake amincewa wasu tsirarun mutane su cigaba da kashe mutane a jiharsa ba.

Umahi yace idan ya sake jin an tada zaune tsaye ko an kashe wasu, to zai kama iyaye, sarakuna da shugabannin yanki da laifi.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN