Buhari ya bukaci N5.23bn na gyaran fadar shugaban kasa a kasafin kudin 2022


Fadar shugaban kasa na bukatar kudi har N5.231,101,743 domin gyaran fadar shugaban kasa tare da gyaran wasu kadarorin da ke ciki a kasafin kudin shekarar 2022 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban majalisar dattawa.

A duban da aka yi wa kasafin kudin, an gano cewa gyaran gine-ginen ofisoshi zai lamushe N5,176,045,297, yayin da ginen gidajen ciki zai kwashe N55,056,446 daga cikin N150,590,609,934 wanda fadar shugaban kasan za ta kashe, Daily Trust ta ruwaito.

A kasafin kudin shekarar 2021, an ware N4,854,381,299 na gyaran injina da kuma kayan wuta a cikin fadar shugaban kasan.

A wannan gyaran da za a yi wa asibitin da ke cikin fadar shugaban kasan, ana tsammanin zai lashe kudi har N21,974,763,310, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda kiyasin ya nuna, gyaran ababen hawa da sassansu zai lashe kudi har N1.6bn idan aka alakanta shi da N436m wanda aka ware domin hakan a kasafin kudin shekarar 2021.

Kusan N180,089,000 aka ware saboda siyan tayoyin ababen hawan da harsasai ba su hudawa, motoci, ababen hawa CCU, manyan motocin daukar kaya, jifa-jifai, motocin asibiti da sauransu.

A shekarar da ta gabata, an ware kudi har N116,194,297 saboda hakan.

Sauya kayan sadarwa na fadar shugaban kasa a wannan shekarar zai lashe N400,000,000.

A kasafin kudin shekarar 2022, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo za su kashe N457,801,260 kan kayan abinci da kuma N301,138,860 da N156,662,400 na kudin cefanensu.


Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar nan ta samu sabbin makamai da za ta iya yakar kowanne nau'in rashin tsaro, TheCable ta ruwaito.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin bikin yaye daliban aji na 68 da suka hada da hafsoshin sojin kasa, ruwa da na sama da aka yi a makarantar horar da hafsoshin soji ta NDA da ke Kaduna.

Shugaban kasan ya bayyana damuwarsa kan rashin tsaro inda ya ce ya sakankance cewa sabbin kayan aiki da aka kawo za su matukar taka rawa wurin inganta tsaro a kasar nan, TheCable ta wallafa.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN