Sanusi Na'Allah mai Olumbo plaza ya sake jawo yan kallo bayan ya hana masu shaguna su bude a Birnin kebbi


Da yammacin ranar Juma'a 8 ga watan Oktoba, Sanusi Na Allah mai kasuwar plaza da ake kira Olumbo plaza a kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin kebbi, ya hana masu shaguna a kasuwar su bude shagunansu bayan Sallar Magariba. Lamari da ya jawo yan kallo har ya kai matsayin wasu matasa suka dinga yin kuwa yayin da aka ganshi yana kokarin kalubalantar wani da ya yi kokarin bude shagonsa.

Wannan dambaruwar ta samo asali ne bayan wata rashin fahimta da ta shiga tsakaninsa da wasu mutane da suka karbi hayan kasuwar kuma suke biyansa kudin kasuwar kai tsaye. Sai dai bayan wasu shekaru, wannan yarjejeniyar ta zo karshe bayan bayanai sun tabbatar cewa Sanusi Olumbo ya karbe kasuwarsa daga hannun wadannan mutane. Sakamakon haka, wannan alaka ta zo karshe.

A shekarun baya, daya daga cikin wadannan mutane yana cikin wadanda suka karbi kasuwar Taushi plaza da ke makwabta da Olumbo plaza. A waccan lokaci haka suka yi sanadin da ya durkusar da kasuwar warwas, kuma suka kashe martabar kasuwar, lamarin da ya sa aka tashi babu dadi tsakanin mai kasuwar Taushi plaza da wadanda suka karbi kasuwar.

Ana zargin cewa wadanda suka karbi wannan kasuwa ta Olumbo plaza, sun dinga yin yadda suka gan dama da kasuwar ba tare da tuntuba, sani, ko amincewar mai kasuwar ba. Kadan daga cikin ababen da ake zargin sun aikata har da :

1. Sayar da shaguna har kudi fiye da miliyan daya ba tare da sanin mai kasuwar ba.

2. Karbar kudaden tallan allon kampanin wayoyin salula da aka sa a kan kasuwar ba tare da sani, ko amincewar mai kasuwar ba.

3. Karbe shagunan mutane da suka ga dama, kuma su sayar da su ga wadanda suke so.

Bayanai sun tabbatar cewa sakamakon haka ne aka shiga kafar wando daya da mai kasuwar.

Sai dai bayanai da muka tattaro sun nuna cewa wasu daga cikin masu shaguna a kasuwar, sun bijire wa bukatar wasu daga cikinsu da ke neman a yi tashin zabbi a bar wa mai kasuwar kasuwarsa.

Yan kasuwar, sun ce da wasu kalilan mutane ne Sanusi Olumbo ke da matsala, amma ba wai ilahirin masu shaguna a kasuwar bane. Sakamakon haka suka bijire wa bukatarsu ta cewa su tashi su bar Olumbo plaza.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN