Lantarki ya kashe barawo bayan ya shiga transfoma domin ya saci manyan wayoyin wuta


Lantarki ya kashe wani barawo bayan ya je yin satar babbar wayar wutar lantarki a wani tarnsfoma da ke shiyar Eric Moore Road, a unguwar Surulere a birnin Lagos.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa barawon da ba a gane ko waye ba, ya mutu ne ranar Talata 5 ga watan Oktoba.

Kazalika wata majiya ta ce barayi sun taba sace babbar wayar wutar lantarki da ke hade da wannan transfomar yan makonni da suka gabata.

Sai dai bayan kampanin Eko Electricity Distribution Company ta sake sa wata waya a transfomar ranar Talata, sai barayin suka biyo dare domin su sake sace wayar inda daya daga cikin barayin ya gamu da ajalinsa nan take saura kuma suka gudu..

An kai gawar barawon gidan ajiye gawaki a birnin Lagos, yayin da yansanda suka fara bincike kan lamarin. 

Previous Post Next Post