Ana yi wa fulani makiyaya kisan gilla a Sokoto


A Najeriya, yayin da ake yawaita zargin fulani da aikata miyagun laifuka a sassan arewacin kasar, musamman kai hare-hare da satar mutane don neman kudin fansa, a yanzu wasu shugabanni fulani makiyaya sun koka kan cewa ana kai harin kai mai uwa da wabi a kan wasu fulanin da basu ji basu gani ba a wasu sassa na jihar Sokoto.

Abubakar Umar, shi ne shugaban kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah, na yankin karamar hukumar Sokoto ta arewa, ya shaida wa BBC cewa, 'yan sa kai na zuwa kasuwannin yankinsu dauke da bindigogi da goruna da kuma adduna, su na samu fulani suna duka da kuma kisa.

Ya ce a takaice dai sai da aka kawo gawar mutum goma sha uku, wadanda aka kashe a kasuwar Mammande, da wasu akalla biyar a garin Giyawa, duk dai a jihar ta Sokoto.

Nasiru Aliyu, shine sarkin yankin fulanin karamar hukumar Sokoto ta Kudu, ya shaida wa BBC cewa, ba a yankin Gwadabawa wannan aika-aika da jami'in sintirin ke yi ta tsaya ba, al'amarin ya shafi kananan hukumomi kamar Tangaza da Gwaranyo.

Ya ce," A wadannan yankuna bafullatani ba shi da ikon shiga motar kasuwa, sai a tsare shi a kashe shi ba tare da bincike a kan ko wanne bafullatani ne, barawo ne ko mugu ne ko ma malami, kudin goro kawai ake yi wa fulani".

Nasiru Aliyu, ya ce 'yan sa kai daukar doka kawai suke da hannunsu suna kashe mana mutanen da basu ji ba su gani ba.

Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar ta Sokoto ta bakin jami'in hulda da jama'ar ta ASP Sanusi Abubakar, ta ce sun samu rahoton abin da ya faru a kasuwar Mammande,

Jami'in dan sandan ya shaida wa BBC cewa, tuni aka gano wasu daga cikin wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Ya ce, ana kuma ci gaba da bincike, wadanda aka kama kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

ASP Sanusi Abubakar, ya ce tuni rundunarsu ta dauki matakai, ba kuma za su gajiya ba, duk wand aka kama da aikata wani abu irin wannan ko makamancin haka ba za a kyale shi ba.

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN