Rahotun 'Takardun Pandora' Gwamna Bagudu, kuskuren hadimansa, ramuwar gayyar yan jarida


Bayan rahotun Jaridar Premium times Hausa kan sakamakon binciken "Takardun Pandora " da ta wallafa ranar 4 ga watan Oktoba, da wadda Jaridar Daily Trust da legit Hausa suka wallafa ranar 5 ga watan Oktoba 2021. Lamari da ya ja hankalin jama'ar Najeriya musamman na jihar Kebbi kan batun. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro wasu bayanai kan lamarin a mahanga na ma'aunin hankali da nazari kan alkiblar da aka fuskanta a halin yanzu. 

Shafin isyaku.com ya tattaro cewa jaridun da suka wallafa labarai rahotun "Takardun Pandora" sun yi ta ambaton sunan Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu fiye da kowane dan Najeriya da aka ambaci sunansa a jerin wadanda ake zargi a wannan rahotu. Kazalika an ambaci sunan kaninsa Alhaji Ibrahim Bagudu har da sunayen wasu kampuna da ake zarginsu su wajen alaka da Bagudu da kaninsa. Sai dai bayan Bagudu, jaridun sun kasa ambaton kampuna, sunayen yan uwa ko wadanda suka taimaka wa sauran yan Najeriya da aka ambata a rahotun "Takardun Pandora" wanda ke nuna cusa ra'ayi kan alkiblar rahotun jaridun domin ci wa wata manufa ko isar da sakon uwayen gida a harkar aikin jarida.

Kurakuren wasu masu taimaka wa Gwamna Bagudu ya taimaka wa rura wutar ware sunansa a rahotun "Takardun Pandora" 

Sakamakon wani bincike da shafin labarai na isyaku.com ya gudanar, ya yi zargin cewa kurakuran wasu na hannun daman Gwamna Bagudu ya taimaka wajen rura wutar yadda wasu jaridu suka dinga fitar da sunan Gwamna Bagudu fiye da sauran yan Najeriya da rahoton ya shafa.

1. Wasu yan jarida suna jin haushin Gwamnati sakamkon wasu kalamai da wani hadiminsa ya yi yan watanni da suka gabata kwanaki kadan bayan dakatar da tsohon shugaban jam'iyar APC na jihar Kebbi. Ana zargin cewa shi wannan hadimin Gwamna Bagudu ya nuna cewa yan jarida a jihar Kebbi ba za su amfana da komi na alkhairi ba matukar basu rungumi tafiya tare da yan soshiyal midiya a jihar ba. Majiyar mu da baya son a ambaci sunansa ya shaida mana, ya ce zance ne da wannan hadimi ya yi a gaban wasu yan jarida.

Sakamakon haka wasu yan jarida suka dauki matakin ba sani ba sabo balle ragowa tunda hadimin Gwamna ya wulakantar da martabarsu ta aikin jarida duk da cewa ko a cikin haka, Gwamna Bagudu ya ba kungiyar yan jarida na kasa NUJ reshen jihar Kebbi tallafin N3m domin jami'an kungiyar su sami halartat babban taronsu na kasa.

2. Halayen wani babban Sakataren Gwamnati na nuna kiyayya karara kan wani Mawallafi kuma.dan Jaridar zamani mai matukar tasiri a jihar Kebbi. Shi wannan Sakataren ya taba cin mutuncin wannan dan jarida a cikin ofishinsa, kuma har wani Dan kanzaginsa dan siyasa ya yi barazanar cewa matukar wannan Gwamnati na kan mulkin jihar Kebbi, ba abin alkhairi da za a yi wa dan Jaridar. Kazalika, wannan Sakataren ya taba nuna cewa baya son ya yi ido biyu da wannan dan jarida lamari da ya haifar da babban gibi ga martabar Gwamnatin dan Bagudu a idanun dan Jaridar da kampani da yake yi wa aiki. 

Ko makircin yan siyasan kudu ne na karya martabar yan siyasar arewa domin ganin dole mulki ya koma kudu a 2023?

Masana na hasashen cewe duba da yadda Gwamna Bagudu ya sami amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mukaminsa na shugaban progressive Governor's forum kuma mai matukar tasiri a siyasar arewa da Najeriya, ba mamaki aka fi nuna shi da yatsa a rahotun "Takardun Pandora", alhalin rahotu ne da ya shafi yan Najeriya da dama ba dan Bagudu kadai ba.

Ko Gwamna Bagudu zai dauki wani mataki?

Shafin labarai na isyaku.com ya yi nazarin lamarin a mahanga na halayen Gwamna Bagudu kan harkokinsa na yau da kullum kamar yadda aka saba. Bayan bullar rahotannin "Takardun Pandora"  a jaridu, Gwamna Bagudu bai ce uffan ba ta kafafen da aka saba isar da sakonsa ga jama'a a jihar Kebbi.

Lamari da ya haifar da zargin cewa wata kila matakin shari'a zai iya biyo baya duba da yadda jaridu suka fuskance shi a wajen rahotanninsu, da kuma neman kare martabar sunansa a idon Duniya. Duba da yadda lamari ya kasance da matar da ake zargin ta aike masa sakon cin zarafi ta wayar salula a 2019, da kuma yadda lamari ya kasance da Mawakan da suka yi masa wakar batanci a 2019, wanda duk matsalolin sun kare a gaban Alkalin Kotu. 

Sakamakon haka ake hasashen cewa watakila ko a wannan lamari, batun zai kare ne a Kotu.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN