Wani barawo ya sace takalman bayan Allah da dama a Masallacin gidan Marigayi Alhaji Inuwa da ke kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin kebbi lokacin da ake cikin gudanar da Sallar Isha'i ranar Laraba 6 ga watan Oktoba.
Ana rokon jama'a Musulmi su taimaka wajen rokon Allah ya tona asirin wannan bara gurbi a cikin al'ummar Musulmi wanda ya raina tare da cin mutuncin Masallacin Allah.
Allah ka yi maganin wannan mugu da ke neman cusa shakka wajen bayin Allah masu yi maka ibada a Masallaci.
Kazalika ana rokon jama'a su sa ido ga duk wanda ya kawo takalma domin sayarwa.