Duba jerin jihohin Najeriya 10 mafi fama da talauci bisa alkaluman binciken BudgIT, 9 na Arewa


Rahoton 'States of States' na 2021 da kamfanin BudgIT ya wallafa ya nuna jerin jihohin Najeriya goma da aka fi fama da bakin talauci da rashin daidaito a Najeriya.

BudgIT wani shahrarren kamfani ne da ya kware wajen bibiyan abubuwan da gwamnatoci ke yi da kudi. 

A rahoton bana, BudgIT ta yi amfani da rahoton hukumar lissafin Najeriya NBS, wajen bayyana jerin jihohin da suka fi fama da talauci.

Sokoto, Taraba, da wasu jihohi takwas ne kan gaba.

Ga jerin jihohi 10 dake kan gaba:

1. Jihar Sokoto - 87.73%

2. Jihar Taraba - 87.72%

3. Jihar Jigawa - 87.02%

4. Jihar Ebonyi - 79.76%

5. Jihar Adamawa - 75.41%

6. Jihar Zamfara - 73.98%

7. Jihar Yobe - 72.34%

8. Jihar Niger - 66.11%

9. Jihar Gombe - 62.31%

10. Jihar Bauchi - 61.53%

Jerin jihohin Najeriya 10 mafi fama da talauci bisa alkaluman binciken BudgIT

Jerin jihohin Najeriya 10 mafi fama da talauci bisa alkaluman binciken BudgIT Source: yourbudgit.com

Dubi cikin rahoton, jihohi 9 cikin 10 na wadannan jihohi na Arewacin Najeriya. Ebonyi kadai ce ta fito daga kudu.

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

Gwamnan jihar Ebonyi, wanda kuma shine Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi, ya bayyana fafutukar Biyafara a matsayin hauka, yana mai cewa mafi yawan masu fada aji a yankin ba sa son shi.

A cewarsa, kaawai abun da duk suke so shi ne a kula da su daidai da sauran yankunan kasar nan.

Gwamna Umahi ya fadi haka ne a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, yayin da ya bayyana a shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin na Channels.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN