Muhimmin halin da ake ciki dangane da zancen Twitter a Najeriya


Dandalin sada zumunta na Twitter, wanda a halin yanzu aka dakatar da shi a Najeriya, ya ce yana fatan za a ba shi damar ci gaba da harkokinsa bayan doguwar tattaunawa.

Bayanin na sa ya biyo bayan sanarwar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi cewa za a dage haramcin da aka yi wa kamfanin na tsawon watanni, amma sai bayan an cika wasu sharudda.Wani mai magana da yawun Twitter wanda ba a bayyana sunansa ba ya fitar da wata sanarwa ranar Juma'a, yana cewa ''Muna ci gaba da hulda da gwamnatin Najeriya kuma mun himmatu wajen tsara hanyar ci gaba don dawo da Twitter ga kowa a Najeriya.''

Ya kara da cewa ''Tattaunawa ce mai muhimmanci da fa'ida - muna fatan ganin an maido da aikin shafin nan ba da jimawa ba. "

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za a iya dage takunkumin da aka sanya wa Twitter, amma sai idan kamfanin fasahar ya cika wasu sharudda.

Amma dokar ta ci gaba da aiki a safiyar Juma'a, duk da cewa Shugaba Buhari ya ce 'yan Najeriya za su iya ci gaba da amfani da dandalin don "kasuwanci da abubuwan da ba su saba wa doka ba".

A jawabin da ya yi na bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya, shugaban ya ce kwamitin shugaban kasa ya yi aiki tare da Twitter kan batutuwa da dama kama daga kan tsaron kasa, zuwa biyan haraji mai inganci da warware takaddama.

Gwamnatin Najeriya dai ta dakatar da ayyukan Twitter a watan Yuni, bayan da dandalin sada zumuntar ya goge wani sakon Twitter da ake ta ce-ce -ku -ce da cewa Shugaba Buhari ya yi wanda ya saba dokokinta.

Sakon ya yi magana game da yakin basasar Najeriya na 1967-1970.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN