Wani da ake zargin cewa barawo ne ya mutu bayan transfoma ta ja shi kuma ta yi bindiga a Festac Town da ke birnin Lagos. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.
Lamarin ya faru ne ranar Juma'a 1 ga watan Oktoba a shiyar 721 Road, G close.
Mazauna Unguwar sun ce an sheda cewa wanda ya mutu ya sha addabar mutanen Unguwar da sace-sace.
Kawo yanzu dai baby Wanda ya dauki alhakin mallakar gawarsa.
Kalli bidiyo a kasa: