Tap di: Mataki da Maigida ya dauka bayan ya kama matarsa tare da abokinsa sumbur a dakin Otel zai baka mamaki


Wani dan kasuwa a kasar Tanzania ya kama matarsa turmi tabarya tare da abokinsa a cikin dakin Otel suna kwanciyar aure. Sai dai matakin da dan kasuwar ya dauka ya ba jama'a mamaki. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Gidan Talabijin na yankin ya labarta cewa dan kasuwan mai suna Issa Kasili dan garin Mpimbwe ne a kasar Tanzania, ya kama matarsa mai suna Mayombi Mwela sumbur tare da abokinsa a cikin wani dakin gidan baki. 

Sai dai marmakin ya fadace su, ya bukaci abokinsa ya biya shi kudin kasar Tanzania Ksh240,000 dai dai da (N892k) kudin Najeriya kasancewa kudin Sadaki da ya biya wajen hidimar aurenta.

An jiyo shi yana gaya wa Mayombi cewa " Ka yi lalata da matata Mayombi, ka biya bukatarka"

Ya gaya wa matarsa cewa:

 "Kin haifa mani.yaro daya kuma yanzu asirinki ya tonu. Ki sani aurenmu ya kare a yau".

Kisili ya gaya wa Mayombi cewa ya dauki matar ta zama matarsa. Ya kuma bukace shi ya biya kudin da ya biya na hidimar aurenta domin yanzu ta zama matarsa.

Bayanai sun nuna cewa nan take Mayombi ya biya Kasili kudin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN