Kungiyar kiristoci na Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama Sheikh Ahmad Gumi.
PFN ta reshen kudu maso yammacin Najeriya tana so a damke babban malamin addinin musuluncin ne saboda maganganun da yake yawan yi.
The Guardian tace kalaman da shehin malamin ya yi kwanan nan, inda yace ka da a ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda ne ya jawo wannan kira.
Kungiyar kiristocin tace babban malamin ya kamata a fara kamawa da zargin alaka da ‘yan bindiga.
Jaridar News Digest tace kungiyar PFN ta dauki wannan matsaya a wajen wani taro da ta shirya a garin Legas a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, 2021.
Archbishop John Osa-Oni ya yi magana Taron ya samu halartar wakilan kungiyar addinin daga jihohin Oyo, Osun, Ondo, Ogun da Ekiti.
Shugaban kungiyar na reshen kudu maso yamma, Archbishop John Osa-Oni yace akwai alamar tambaya a game da kalaman da ke fitowa daga bakin shehin.
Archbishop John Osa-Oni yace da a ce Sheikh Ahmad Gumi jagoran addinin kirista ne, da tuni an kama shi. Faston ya na mai nuna akwai son kai a lamarin.
Da yake jawabi a madadin Pentecostal Fellowship of Nigeria, John Osa-Oni yace ya kamata gwamnatin tarayya ta kama malamin domin a hukunta shi.
A na sa bangaren, babban faston nan na Legas, Dr. Alfred Martins, ya yi kira ga gwamnati tayi bakin kokarinta wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Legit Hausa
Rubuta ra ayin ka