Ƴan bindiga sun 'sa wa garuruwa 20 wa'adin biyan haraji' a Sokoto


Yankin karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto a Najeriya ya koma karkashin ikon 'yan bindiga ta yadda suke cin karensu ba babbaka da sanya wa jama'a haraji, a cewar a mazauna yankin.

Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Arewa, Honorabul Aminu Boza, ne ya tabbatar da haka a tattaunawar da BBC ta yi da shi.

Ya ce kamar yadda suka sha fada duniya ta sani, karamar hukumarsu ta Sabon Birni ba ta karkashin ikon gwamnatin Najeriya, tana hannun 'yan bindiga ne, domin su suke yin yadda suke so da al'umma.

Ya kara da cewa a halin da ake ciki 'yan bindigar sun sanya wa garuruwa sama da ashirin wa'adin biyan kudin fansa kuma zuwa yanzu sama da goma sun biya, yayin da wasu suka biya rabi saura rabi.

Kudin fansar sun kama daga naira dubu dari biyar zuwa naira miliyan biyu har naira miliyan hudu.

Kuma 'yan bindigar sun bai wa garuruwan wa'adin sati biyu ne na su biya kudaden, inda wa'adin kamar yadda dan majalisar ya ce a ranar Juma'a 29 ga watan nan na Oktoba zai kare.

Alhaji Aminu ya ce duk mutanen garin da ba su biya kudin da 'yan bindigar suka yanka musu ba zuwa wa'adin na ranar Juma'a to lalle ba abin da ya rage musu illa su jira mutuwarsu kawai.

Dan majalisar ya ce gaba-gadi 'yan bingidar suke zuwa a babura su tsaya a bayan gari, su aika masu babura biyu a dauko masu garin, kamar mai unguwa da limamin gari su gaya musu cewa,

"Idan suna so su zauna lafiya to su hada kudi kaza, su na mai tabbatar musu cewa su ne gwamnati a yanzu."

Honorabul Aminu ya ce duk hukumar da take a Najeriya ba wadda ba su sanar wa da halin da suke ciki ba, domin daman a sansanoni biyar da aka sa jami'an tsaro a yankin karamar hukumar tasu ta Sabon Birni, a yanzu babu ko daya idan ba cikin garin Sabon Birni ba.

Ya kara da cewa hatta cikin garin ma bai tsira ba, domin a kwanakin baya barayin dajin sun shiga unguwar na dawaki, wadda ke cikin garin sun kama mata da maza sai da aka biya kudin fansa sannan suka sako so.

Ya ce ko a ranar Talatar nan 26 ga watan nan na Oktoba 'yan bindigar sun hallaka wajen mutum bakwai a hare-haren da suka kai yankin.

Daga cikin hare-haren barayin sun tsare wata babbar hanya ta Tsamaye wadda ake bi zuwa Isa da Shinkafi da Katsina da Nijar, wanda a lokacin suka kashe shugaban wata makarantar sakandire da wani dan gwagwarmaya Lawwali Kakale, bayan kuma sauran mutanen cikin motar da aka kashe mutanen, wadanda ke kwance a asibiti.

Dan majalisar ya ce yanzu bayan halin da suke ciki na wannan matsalar tsaro, fargabarsu kuma ita ce wadanda suke maganar mawuyacin halin da ake ciki irinsu su ake neman a kassara, saboda ba a jin dadin yadda suke fitowa suna magana a kai.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan dan majalisa ke fito fili yana bayyana cewa 'yan bindiga sun kame iko da yankin na Sabon Birni ba, domin ko a watannin baya, shi da takwaransa da ke wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu honorabul Sai'du Ibrahim sun sheda wa BBC haka.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN