Da duminsa: Yan bindiga sun sake aikata wani mugun aiki kan bayin Allah a Zamfara, duba abin da ya faru


Tsagerun yan bingida sun sake kai farmaki ƙauyen Yanbuki dake ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara. Punch ta ruwaito cewa maharan sun hallaka aƙalla mutum bakwai sannan sun kwashi kayan abinci, tare da yin awon gaba da dabbobi sama da 1,500.

Wani ɗan asalin ƙauyen, Garba Musa, wanda ya zanta da manema labarai a Gusau, yace adadi mai yawa na yan bindigan sun mamaye ƙauyen ranar Talata da daddare. 

Musa ya bayyana cewa da isowar su ƙauyen, sai suka buɗe wuta kan duk wanda suka gani domin tsorata mutanen dake garin. /

Yadda lamrin ya faru Musa yace: "Suna isowa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi saboda haka kowa ya fara gudun neman tsira da rayuwarsa." 

"Daga nan kuma sai suka fara shiga gida-gida suna neman kayan abinci da dabbobi, sannan kuma duk shagon da suka gani suna fasa shi su kwashi kayan abinci." 

"Hakanan kuma sun yi awon gaba da dabbobin kiyo sama da 1,500, wanda suka haɗa da shanu, awaki da tumaki." Mutum nawa yan bindigan suka kashe? 

A cewarsa bayan yan bindigan sun gama abinda suka zo yi, an gano mutum 7 sun rasa ransu sannan wasu da dama sun jikkata, kamar yadda Channels ta ruwaito.

 "Mun yi jana'izar mutum 7, kuma adadin waɗanda suka mutu ba zai wuce haka ba, domin wasu sun tsere cikin daji domin tsira da rayuwarsu." 

/Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka? Kakakin yan sandan jihar, SP Muhammed Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamrin ga manema labarai, yace: 

"Kwamishinan yan sandan jihar ya tura ƙarin jami'an yan sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya." 

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN