Jiragen yakin soji sun yi luguden wuta a dajin Kaduna, duba abin da ya faru da yan bindiga


Hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce jiragen yaki sun yi luguden bama-bamai a dajin Kwaga cikin yankin Birnin Gwari inda suka kashe akalla 'yan fashin daji 40.

Hedikwatar ta kuma ce a yayin hare-haren ta sama an kuma lalata mab'oya da sansanonin 'yan fashin da dama a jihohin Kaduna da Katsina da kuma Sokoto.

Kazalika an kuma kama wasu gaggan 'yan fashin daji da suka yi k'aurin suna a Dajin Dangulbi na jihar Zamfara.

Cikin 'yan fashin dajin da kuma masu tsegunta musu bayanai da ke cikin jerin wad'anda jami'an tsaro ke nema kuma, hedikwatar tsaron Nijeriyar ta ce daga farkon watan Oktoba na 2021 zuwa tsakiyarsa, dakarunta sun kama Mamuda Aliyu Dangulbi, da Rilwan Sani Dangulbi, da Yusuf Adamu Dangulbi, da kuma Yakubu Umar Maihaja, dukkansu a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

A yayin hare-haren na jami'an tsaro an kuma kubutar da fararen hula da aka sace tare da gano makamai da alburusai.

Sanarwar hedikwatar tsaron wadda Birgediya Janar Benard Onyeko, ya fitar ta kuma ce dakarun tsaro sun samu gagarumar nasara kan 'yan fashin daji a hare-haren baya-bayan nan a yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna da dazukan Meshema da 'Yan Fak'o da Gebe da Gatawa na jihar Sokoto da kuma dajin Rugu na jihar Katsina.

Haka zalika sanarwar ta tabbatar da kashe 'yan Boko Haram da dama da kuma kama wasu a cikin watan Oktoban, a daidai lokacin da ta ce 'yan ta-da-kayar-bayan da suka tuba tare da iyalansu, na ci gaba da ajiye makamansu kana suna mik'a wuya ga dakarun tsaro.

Yankunan da aka samu irin wannan nasara akwai titin Gwoza zuwa 'Yantake zuwa Bita sai titin Gwoza zuwa Farm Center zuwa Yamtake da kuma tsaunin Mandara da garuruwan Pulka da Hambagda duka a jihar Borno.

A cewarta zuwa yanzu jimillar 'yan ta-da-kayar-baya dubu 13, 243 ne suka mik'a wuya.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN