An tuhumar wani mutum dan kasar Kenya, Stephen Nyangeri Mauti, da laifin kisa saboda halaka matarsa, Faith Nyatichi, saboda ta fada masa bata gamsu da shi ba bayan sun yi kwanciyar aure.
Lamarin, a cewar k24tv, ya faru ne a Kangemi a yankin Kangemi da ke Nairabi a ranar 3 ga watan Oktoban 2021, kamar yadda LIB ta ruwaito.
Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciya
A cewar rahoton da aka karanto a kotu a ranar Alhamis 14 ga watan Oktoba, marigayiyar ta ziyarci unguwar Kangemi Hill inda suka kama hayar gida bayan baro Nyeri inda suke zaune a matsayin mata da miji tun Agustan 2021.
An ruwaito cewa marigayiyar ta bar gidan mijinta ta shaida masa za ta tafi ziyartar 'yar uwarta a Kiserian kuma bayan wani lokaci da bata dawo ba sai ya kira amma ta fada masa ta tafi kauye.
Wani sashi na rahoton ya ce:
"Bayan zurfafa bincike, wanda ake zargin ya gano matarsa bata da 'yan uwa a Kiserian kuma ba kauye ta tafi ba."
Wanda ake zargin ya kuma tambaya yayan matarsa wanda ya tabbatar masa ba su da 'yan uwa a Kiserian.
Dalilin da yasa matar ta dawo gidan mijin
Rahoton ya bayyana cewa a ranar 1 ga watan Oktoba, matar ta kira mijinta a waya ta ce zata kai masa ziyara tunda ba shi da lafiya.
Ta cika alkawari, ta ziyarce shi, da isarta, ta dafa abincin rana suka ci tare, sai suka fita tattaki a kusa da kasuwar Kangemi sannan suka koma gida. Matar ta yi abincin dare, suka ci sannan suka kwanta barci.
A cewar rahoton yan sanda, sun tattauna amma ba su cimma matsaya ba tunda marigayiyar kuka ta rika yi don haka suka yi kwanciyar aure sannan suka yi barci.
A ranar 3 ga watan Oktoba, sun tashi sannan matar ta dafa abincin safe, a yayin da suke shan shayi, wanda ake zargin ya yi kokarin shawo kanta kada ta rabu da shi ta auri wani daban.
A jawabin da ya yi wa yan sanda, wanda ake zargin ya ce ya nemi ta fada masa gaskiya kan zargin cewa tana zaman dadiro da wani mutum daban. Ya ce daga nan ta fara masa ihu tana cewa shi ba cikakken namiji bane bayan kwanciyarsu.
Kamar yadda ya zo a ruwayar LIB, wanda ake zargin ya ce ya damke ta ya rufe mata baki don ta dena yi masa ihu.
Ya ce ya yi tsamanin ta hakura ta dena masifar ne a lokacin da ta yi shiru amma sai ya lura ta suma. Ya kira makwabta sun garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar ta rasu.
Babban Majistare na Nairabo, Bernard Ochoi ya bada umurnin a yi wa wanda ake zargin gwajin kwakwalwa kafin a yanke masa hukunci a ranar 17 ga watan Oktoban 2021.
Matar wacce musulma ce mai sanye da hijabi ta sanar da mijinta, Bakhriddin Azimov cewa likitan fatar dan asalin kasar Rasha, Vladimir Zhirnokleev ya yaba kyawun fatarta.
Daga nan ne mutumin ya kai wa likitan farmaki, yanzu haka yana fuskantar hukunci akan cin zarafi kamar yadda LIB ta ruwaito.
Source: Legit.ng