Yadda fusatattun jama suka yi wa soji dukan ajali saboda ya kashe yarinya mai shekara 3, duba yadda ta faru


Fusatattun jama'a sun kashe wani sojin jandarma a yankin Molyko da ke makwabtaka da Buea da ke kudu maso yammacin kasar Cameroon bayan jandarman ya kashe wata karamar yarinya mai shekara uku da haihuwa domin mahaifiyarta bata bashi cin hanci ba.

Rahotanni sun ce jandarman ya kashe yarinyar mai suna Minex Kimora bayan mahaifiyarta ta ki ta bashi cin hanci 500f da ya bukata.

Mahaifiyar yarinyar tana kan hanyarta domin ta kai diyarta makaranta da safe ranar Alhamis 14 ga watan Oktoba, amma sai jandarman ya tsayar da su a wajen wani shingen tsaro. Sai dai yayin da mahaifiyar yarinyar ke shirin gyara tsayuwar motarta a kan titi, sai jandarman ya yi harbi da bindigarsa.


Sakamakon haka harsashi ya fasa gilashin baya na motar ya sami yarinyar da ke zaune a cikin motar. Lamari da ya yi sanadin mutuwar yarinyar nan take.

Sakamakon haka fusatattun matasa suka far wa jandarman, bayan sun wulakanta shi, sun kuma yi masa dukan ajali. Daga bisani suka dauki gawar yarinyar suka kaita ofishin shugabanci na garin.

Sai dai an karo jami'an tsaro, kuma harbe harbe ya kaure, lamari da ya yi sanadin tarwatsewar masu zanga zanga.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN