Da duminsa: Dubun wasu Lakcarori biyu dake neman ɗalibai mata da biɗala ya cika, An sallamesu daga aiki


Hukumar zartarwa na kwalejin fasaha ta tarayya dake Bauchi, ta amince da korar wasu malamai biyu, Malam Abubakar Baba da Adebusoye Sunday, bisa zargin cin zarafin ɗalibai mata. 

Shugaban kwalejin, Mr Sunusi Gumau, shine ya sanar da hukuncin korar malaman bayan taron su karo na 98, ranar Lahadi a Bauchi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito. 

Gumau ya kara da cewa majalisar zartarwan kwalejin ta ɗauki wannan matakin ne bayan gudanar da bincike kan lamarin wanda kwamitin da aka kafa ya yi. 

Shin matakin ya yi dai-dai? Ya kuma bayyana cewa malaman biyu, dukkan su suna koyarwa ne a kwalejin a wasu sashin kwasa-kwasan makarantar. 

The cable ta rahoto Shugaban kwalejin yace: "Wannan matakin shine na ƙarshe da zamu iya ɗauka game da malaman mu da ake zargi da neman ɗalibai mata." "Lamarin Abubakar Baba ya zo mana ne a ranar 4 ga watan Augusta. 

A dokar makarantar mu, idan irin haka ta faru dake zaki rubuta wasika ga hukumar makaranta, kuma ɗalibar ta yi haka." "Bayan haka mun tambayi lakcaran, amma bai bamu gamsasshiyar amsa ba, saboda haka muka kafa kwamitin bincike. 

Bayan bincike da shawarwarin kwamiti a yau mun sallami Abubakar Baba daga aiki a kwalejin fasaha ta tarayya dake Bauchi."

Gumau ya kara da cewa hukumar makaranta ta sallami mista Sunday daga aiki a kwalejin fasahar nan take. Shugaban kwalejin yace an gabatar da kwakkwaran shaida dake nuna Sunday ya ci zarafin ɗalibar shi a makarantan. Daga ƙarshe ya kara tabbatar da cewa daga yanzun lakcarorin biyu ba ma'aikatan kwalejin bane, kuma za'a mika takardar kora ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace. 

Source: Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN