Yanzu-yanzu: Ganduje ya bawa fasihin makaho aikin koyarwa a Kano


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bawa Dahuru Idris Abdulhamid, makahon malami da ke koyarwa kyauta a jihar aikin yi.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan Daily Trust ya wallafa wani rahoto game da Dahuru, hakan yasa mutane da dama suka san shi.

Duk da makaho ne, Dahuru, wanda ya yi karatu, ya kasance yana bada gudunmawarsa ga al'umma ta hanyar koyarwa.

Da Duminsa: Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take

Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take. Hoto: Daily Trust Source: Facebook

Bayan Daily Trust ta wallafa labari game da shi a ranar 25 ga watan Satumban 2021, wani mai tallafawa al'umma ya siya masa gida mai daki hudu.

A wani hira da aka yi da shi a karshen mako, Dahuru ya mika godiyarsa amma ya yi kira ga gwamnati ta taimaka ta bashi aiki na dindindin.

Gwamnatin jihar Kano, ta bakin kwamishinan ta na ilimi, Muhammmad Sanusi Sai'id Kiru, ta tuntubi Dahuru a ranar Asabar bayan fitar rahoton a kansa.

An gayyaci Dahuru gidan gwamnatin Kano, inda ya gana da Ganduje.

An rahoto cewa gwamnan ya tambayi matashin makohon malamin abin da ya ke so gwamnati jihar ta yi masa, sai ya nanata rokonsa ba baya na neman a bashi aikin gwamnati na dindindin.

Ganduje, daga bisani, ya bada umurnin a bawa Dahuru aikin koyarwa na dindindin a makarantar mutane masu bukata na musamman da ke Tundun Maliki a mataki na 7(2).

Wannan ce makarantar da Dahuru ya yi karatunsa na frimari da sakandare.

A halin yanzu Dahuru yana karatu a jami'ar National Open University of Nigeria (NOUN) inda Farfesa Uba Abdallah, tsohon shugaban jami'ar ya biya masa.

Kazalika, bayan fitar da bidiyon hira da aka yi da shi, gidauniyar Near ta dauki dawainiyar biyansa N10,000 duk wata a matsayin kudin mota har ya kammala karatunsa a NOUN.

Ku saurari karin bayani ...

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN