Yan Taliban sun kashe wata yarinya mai suna Mahjabin Hakimi wacce ake matukar martabawa a kungiyar kwallon Municipality Volleyball Club da ke Birnin Kabul, suka kuma saka hotunan jikinta a shafukan sada zumunta. Shafin isyaku.com ya samo.
Kocinta mai suna Suraya Afzali ta gaya wa Jaridar Persian Independent a wata tattaunawa. Ta ce tun farko wannan wata ne yan Taliban suka kashe yarinyar, sai dai sai a wannan lokaci ne labarin ya bulla, saboda yan Tiban sun tsoratar da yan uwa da iyayenta cewa za su kashe duk wanda ya fitar da zancen.
Ta ce yan Taliban sun kasheta ne bayan ta kasa tserewa daga kasar Afghanistan bayan Taliban ta kwace mulkin kasar.
Taliban da ta kafa sabuwar Gwamnati a Afghanistan ta haramta wa mata yin wasannin motsa jiki, ciki har da kwallon kafa, volley ball da cricket. Ta ce ba dole ne mata su yi wadannan wasnni ba.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI