Jami'an tsaro sun kama akalla Karuwai guda 27 sakamakon wani samame da suka kai a wasu Otel Abuja.
Wani jami'i mai sunu Sani Amar, wanda shine Mataimakin Daraktan jindadi da walwala na FCT Social Development Secretariat, ya ce an yi Kamen ne domin kare lafjyar al'umma mazauna Birnin.
Ya ce an aiwatar da samamen ne bisa umarnin Ministan birnin tarayya bisa la'akari da barazana da wannan harkar ke jawowa a tsakanin jama'a a birnin.
Ya ce an kama akalla Karuwai guda 27 kuma an mika su ga hukumar yansanda domin gurfanar da su a gaban Kotu.
Rubuta ra ayin ka