Type Here to Get Search Results !

Rana irin ta yau aka kashe Framinista Indira Gandhi a kasar India, duba dalili da yadda aka kasheta


An kashe Firaministan kasar India Indira Gandhi da karfe 9:29 na safiyar ranar 31 ga watan Oktoba 1984 a gidanta da ke Safdarjung Road a birnin New Delhi da ke kasar India. Shekara 37 kenan ranar 31 ga watan Oktoba 2021.

Masu tsaron lafiyarta mabiya addinin Sikh masu suna Satwant Singh da Beant Singh sun buda mata wuta da bindigogi inda suka yi mata ruwan harsashi.

Lamari da ke da alaka da wani aikin da sojin kasar India suka yi da ake kira Operation Blue Star. Aikin da suka gudanar tsakanin 1 zuwa 8 ga watan Yuni 1984, wanda Praminista Gandhi ta bayar da umarnin gudanarwa.

Gandhi ta ba soji umarnin cire wani shugaban Addinin Sikh mai suna Jarnail Singh Bhindranwale tare da mabiyansa daga wajen bauta da suke matukar martabawa a Harmandir Sahib da ke Amritsar a jihar Punjab. 

Lamari da ya haifar da mutuwar masu yin aikin hajjin Sikh da dama tare da yin dameji ga Akal Takht.

Wannan lamari da sojin kasar India suka yi ya haifar da korafe-korafe a ciki da wajen kasar India. Sakamakon haka aka sami mumunar tarzoma da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane a kasar.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies