Saboda yin kida wajen biki yan Taliban sun aikata mugun aiki kan bayin Allah


Wasu 'yan bindiga sun harbe wasu baki 'yan biki biyu tare da jikkata wasu a garin Nangarhar da ke gabashin Afghanistan, saboda kida da aka sa a wurin bikin.

Ba a dai gane ko su wane ne 'yan bindigar ba, amma wasu mutnen yankin sun ce mayakan Taliban ne, abin da ita kuma Taliban ta musanta.

Wasu da aka yi abin a kan idonsu sun gaya wa BBC cewa ana bikin aure ne hudu a tare ranar Juma'a da dadre, kuma iyalan da ke bikin sun nemi izini daga wani jagoran Talibn na yankin domin sun sanya kida a wurin bikin wanda mata ne kawai ke halarta.

Ana cikin bikin ne sai kawai cikin dare 'yan bindiga suka kutsa ciki suka yi kokarin farfasa lasifika da saurn kayayyakin da aka kuuna kidan.

Da iyalan suka ja da yan bindigar sai kawai suka bude wuta, inda suka kashe baki biyu tare da jikkata wasu goma da suka hada da yara.

Ba a dai gane ko su wye 'yan bindigar ba, amma wasu mutanen yankin sun ce mayakan Taliban ne, abin da shi kuma kakakin Taliban din - Zabihullah Mujahid - ya musanta, amma kuma ya ce ana gudanar da bincike a kai:

Jana'iza

Ya ce zuwa yanzu ba su yadda abin ya faru ba. Matsala ce ta tsakaninsu ko kuwa?

Ya ce su a tsarinsu, ba wanda yake da ikon hana wani jin kida ko wani abu, sai dai kawai a yi kokarin shawo kan mutum ya bari.

Wannnan ita ce hanyarsu. Duk wanda ya kashe wani da kansa, ko da jami'insu ne to wannan laifi ne, za su gabatar da shi ga kotu a yi masa hukunci.

Amma kuma idan wani mutum ne daban, to wannan wata matsala ce ta daban da ba su damu da ita ba, saboda suna fuskantar irin wannan matsala da yawa a kusan kullum, ko kuma ba kullum ba, a ce a duk mako. Idan ta faru a yau to za su yi kokarin ganin sun dakatar da ita a nan gaba.

Asibiti
ASALIN HOTON, REUTERS
Wasu dai na ganin ba wasu 'yan bindiga da za su aikata haka a wannan gari na Nangarhar idan ba 'yan Taliban din ba, domin an sha zarginsu da aikata hakan a baya.

A baya a lokacin da 'yan Taliban din na rike da gwamnati, sun sanya tsauraran dokokin hana jin kida. Kuma tun lokacin da suka dawo mulki a watan Agusta, an zarge su da kisan mawaki da farfasa kayan kade-kade

Abin da ya sa da yawa mawaka suka gudu daga kasar.

A watan Agust kungiyar IS ta taba kai harin bam a yayin wani biki a Kabul, abin da ya yi sanadin hallaka mutum 63 tare da raunata sama da 180

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN