Dakatar da FB: Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi


Kamar yadda Yahoo Finance ta ruwaito, wannan lamarin da ya auku a ranar ranar Litinin 3 ga watan Oktoban 2021.

Dakatar da kafar ya janyo gabadaya dukiyar Zuckerberg ta sauka zuwa $121.6bn, yayin da ya sauka kasan Bill Gates inda ya koma na 5 a cikin jerin biloniyoyin duniya, ya sauka daga $140bn.

Dama Wall Street Journal ta fara wallafa akan illolin Facebook da sauran kafafe

A ranar 13 ga watan Satumba, Wall Street Jornal ta fara wallafa labarai akan yadda Facebook take sane akan illar da take yi wa yara mata masu karancin shekaru kamar yadda Instagram ma take yi.

Rahotannin sun janyo hankalin gwamnati kafin a wayi gari a ranar Litinin duk su ka dena aiki.

A wata tattauna da aka yi da Frances Haugen, tsohon ma’aikaciyar gyara akan ingancin Facebook, ta bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa Facebook ta san illar da take kawowa.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, DW ta bayyana, kamfanin na sane da illar da take kawowa musamman ga yara kanana da suke amfani da Instagram wurin bayyana tsiraicin su, ga duniya.

Kamar yadda Haugen ta bayyana:

“Na ga irin illar da kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook suke haifarwa.”

“Irin Facebook din da ake yi yanzu ya na lalata mana yara kuma su na kawo illa ga dabi’u da al’adu a duniya.”

Sai dai a bangaren Facebook, sun bayyana cewa an dan samu wata matsala ne kuma kowa ya san za a iya samun irin wannan matsalar.

“Zai fi dacewa jama’a su fahimci cewa akwai yuwuwar a samu matsala da fasaha ko kuma wata ta daban,” kamar yadda Nick Clegg, mataimakin harkokin Facebook na duniya ya bayyana wa CNN.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN