Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa


Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar damkar masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kudin fansar yaro dan shekara 7, kamar yadda The Punch ta ruwaito,

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin inda ya ce sun kama wani Muhammed Abubakar mai shekaru 42 da Clinton Niche mai shekaru 18.

Hakan ya biyo bayan korafin da aka kai ofishin ‘yan sandan na Agbara

Oyeyemi ya ce mahaifin yaron, Stephen Ajibili, ya kai korafin satar dan sa, Daniel, da aka yi inda ya ce mahaifiyar sa tana tsaka da aiki da misalin karfe 11:20am aka sace shi.

Ya kara da bayyana cewa mahaifin yaron ya bayyana mu su yadda masu garkuwa da mutanen su ka kira kuma su ka bukaci kudin fansa N1m.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, ya ce:

“Bayan an kai rahoton, kwamandan ‘yan sandan yankin Agbara, CSP Kayode Shedrack, ya yi gaggawar tattara rundunar ‘yan sanda don su yi gaggawar bincike da daukar mataki akan lamarin.

“Kokarin ‘yan sandan ya haifar da da mai ido don masu garkuwa da mutanen sun bukaci iyayen yaron su kai kudin fansa daga nan aka dana musu tarko.

“Daga nan ne ‘yan sanda su ka tasa keyar su har sai da su ka nuna musu inda su ka daure yaron a cikin daji.

“Yayin tambayar wadanda ake zargin, sun sanar da ‘yan sanda cewa su 3 ne, dayan ya na kula da inda aka daure yaron ne yayin da su kuma su ka je amsar kudin fansa.

“Bayan fahimtar an kama mutane 2 daga cikin su, daya ya ba hammatar sa iska take yanke.”

Jami’in hulda da jama’an ya ce mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar, DCP Abiodun Alamatu, ya bayar da umarnin yin gaggawar mayar da wadanda ake zargin zuwa yankin yaki da garkuwa da mutane na bangaren binciken sirri na laifuka manyan laifukar rundunar.

Danny Manuel, mai magana da yawun hukumar NSCDC a Enugu ya ce an kama mutumin dauke da katin ATM uku, wayoyin salula biyu, wani ganye da ake zargin wiwi ne da wani bindiga na gargajiya.

Ya ce sunan wanda ake zargin Manuel Oguamanam da aka kama a WTC Estate a Enugu misalin karfe 2 na rana bayan dalibai da ke dawowa daga makaranta sun hange shi yana yi wa wasu fashi da bindigarsa pistol.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN