Mutumin da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu a Sweden ya mutu


Mai hada fina-finan Cartoon, Lars Vilks dan kasar Swedin ya gwabza mummunan hatsari duk da ‘yan sanda sun ci gaba da ba shi tsaro tun shekarar 2007 da yaci zarafin mazon Allah, Muhammad SAW, sai ga shi ya halaka sanadin hatsarin mota.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, tsohon mai shekaru 75 ya mutu tare da ‘yan sanda 2 da suke ba shi tsaro na musamman bayan motar su ta gwabza karo da wata babbar mota a ranar 3 ga watan Oktoba kamar yadda ‘yan sandan Swedin suka tabbatar wa da AFP.

Lars Vilks: Mutumin da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu a Sweden ya yi ƙazamin hatsarin mota ya mutu

Lars Vilks wanda ya yi cartoon din batancin Annabi Muhammadu ya yi hatsari ya mutu. Hoto: The Guardian Source: Facebook

LIB ta ruwaito yadda kakakin rundunar ‘yan sanda ya bayyana cewa:

“Anyi bincike kamar yadda ake yi wa sauran hatsarorin kan hanya. Saboda har ‘yan sandan da ke tsaron sa sun halaka kuma yanzu haka an samar da bangaren bincike na musamman akan lamarin.”

Babu wanda ake zargin ya na da alhakin hatsarin

Ya kara da bayyana cewa babu wani mutum da ake zargin ya na da alhaki akan lamarin.

Hatsarin ya auku ne a kusa da wani gari, Markaryd yayin da motar Vilks ta afka wa wata babbar mota. Duk motocin sun kama babbaka da wuta kuma yanzu haka direban babbar motar yana asibiti.

Ba a gano musababin wutar ba

A takardar, ‘yan sanda sun bayyana cewa ba a gano dalilin kama wutar da motocin su ka yi ba.

Kamar yadda shugaban rundunar ‘yan sandan yankin, Carina Persson ya ce har ‘yan sanda 2 da suke kula da shi sun halaka.

Tun 2007 ake kulawa da Vilks bayan ya ci zarafin manzon Allah Muhammad SAW, inda ya hada wani hoto da jikin kare ya alakanta shi da ma’aiki. Hakan ya janyo tashin hankali ga musulmai.

Har Al-Qaeda ta sa $100,000 ga duk wanda ya halaka Vilk.

Tashin hankalin da ya janyo har firayim ministan kasar Sweden, Fredrik Reinfeldt ya yi taro na musamman da jakadan kasashen musulmai musamman akan lamarin.

A shekarar 2015 ne Vilks ya sha da kyar daga farmakin da aka kai ma sa da bindiga a wani taro da su ka yi a Copenhagen wanda ya yi sanadin halaka wani direktan fina-finai.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN