Da za a sake zaɓen gwamna a Kano APC faɗuwa za ta yi


Wasu gaggan 'yan jam'iyyar APC mai Mulki a Kano sun kai korefe-korafe ga shugaban jam'iyyar na rikon kwarwa, gwamna Mai Mala Buni dangane da abin da suka kira da neman yi wa jam'iyyar kanshin mutuwa a jihar.

A ranar Talata ne wasu ƙusoshin jam'iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha'aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam'iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam'iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.

Honorabul Sha'aban ya bayyana wa BBC cewa jam'iyyar ta APC a jihar Kano na ƙara nutsewa a ruwa shi ya sa suka ga ya dace su ɗauki mataki saboda gujewa alhaki.

"Mun faɗi abubuwa kamar uku - gaba ɗaya zaɓen da ake cewa an yi daga bangaren gwamnati na shugabannin jam'iyya daga kananan hukumomi da mazaba, mun yi watsi da shi kuma ba mu san shi ba.

"Saboda an dora mutanen da ba su cancanta ba, an cire mutanen da suka dace. Haka ma a zaben ƙananan hukumomi," a cewar Sha'aban Sharada.

Ya bayyana haka a matsayin rashin adalci kuma ya ce abin da ya ja wasu suka fusata kenan suka gudanar da nasu zaɓen daban da na gwamnati.

Ya kuma bayyana cewa da shi da mutanen da suka kai wa Mai Mala Buni ziyara sun barranta kansu daga zaben da gwamnati ke shirin gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa.

"Da yawa daga cikin ƴan majalisar jihar Kano, har ma da mutanen da ke aiki da gwamnati kamar kwamishinoni idan ka keɓe da su suna faɗin maganganu marasa daɗ. Mu dai so mu ke a gyara don lokaci bai ƙure ba," in ji shi.

Honorabul Sha'aban Sharada ya musanta batun cewa shigo-shig ba zurfi suke yi wa gwamnatin jihar Kano ta yanzu.

"In da so muke ta ɓare waɗannan jajirtattun mutane da suke cikin wannan tafiya da sai su yi shiru su riƙe hannunsa (gwamnan Kano) su yi shiru har sai lokacin zaɓe, kamar yadda ragowar ƴan uwanmu su ka yi shiru," a cewarsa.

Honorabul Sha'aban ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta daina farin jini a jihar Kano kuma da za a gudanar da zaɓe a yanzu ba ta yi nasara ba. "In yau za a yi zaben gwamna a Kano, APC faɗuwa za ta yi. Mu kuma ba ma so ta faɗi," in ji shi.

Honarabul Sha'aban ya ce Mai Mala Buni ya saurare korafin da su ke je da shi.

Sai dai ya ce yana kyautata zaton dama shugaban jam'iyyar na da masaniya kan abubuwan da ke faruwa dama yana jira ne a kai masa korafin.

"Na yi imani mutum ne adali da bai jin tsoron komai kuma zai yi gaskiya," a cewarsa.

Haka kuma ya ce ko shugabancin jam'iyya bai yi komai kan lamarin ba, da shi da sauran mutanen da suka kai wa shugaban jam'iyyar ƙorafi sun fita har a wurin Allah.

Shugaban riƙo na jam'iyyar APC a Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC cewa sun ji mamakin wannan taron da aka yi.

Ya bayyana cewa su ba su da wata damuwa game da wannan taron kuma zaɓe za a yi a ƙarshen mako kuma duk wanda ya samu nasara za a ba shi dama ya ja ragamar jam'iyyar a matakin jiha.

"Jam'iyyar APC haɗaka ce, kuma kowanne ɓangare an ba shi muƙami daidai da su bisa adalci," in ji Abbas.

Shugaban na riƙo ya ƙara da cewa sun ji mamaki yadda Malam Ibrahim Shekarau ya halarci taron da aka yi a ranar Talata.

A watannin da suka wuce ma sai da wani ƙusa a jam'iyyar APC, Dan Balki Kwamanda ya caccaki salon jagorancin APC a Kano inda ya ce ba za su zura ido a dunga kama-karya ba a cikin jam'iyyar.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN