Matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi magana mai muhimmanci kan Matan Gwamnoni


Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta yi kira ga manema labarai da su rinka bayyana ɗumbin ayyukan da matan gwamnoni ke yi wa al'umma.

Punch ta rahoto cewa ta yi wannan kiran ne ranar Laraba da daddare, a wurin taron karrama matan, waɗanda suka taka rawa a rayuwar mutane, musamman talakawa.

Aisha, wadda ta kasance bakuwa ta musamman a wurin taron, ta samu wakilcin, Aliyu Abdullahi, mak taimaka mata ta ɓangaren yaɗa labarai da hulɗa da jama'a.

Matar shugaban ƙasa tace:

"Naji daɗi da aka gayyace ni wannan taron, wanda ak shirya domin karrama mata bisa kokarin da suke ga al'umma."

"Ina son yin amfani da wannan damar wajen kira da kafafen watsa labarai da sun rinka bibiyar matan shugabanni domin watsa ayyukan alherin da suke."

"Haɗin kai tsakanin waɗannan ɓangarorin biyu nasara ce kan nasara kowa zai samu damar sauke nauyin dake kansa, matan sun yi aiki, manema labarai sun watsa."

Aisha ta yaba wa waɗanda suka shirya taron

Matar shuagaban ta yaba wa shugabannin gidan jaridar da suka shirya taron karrama gwarazan matan gwamnoni.

Ta kuma ƙara da cewa wannan zai taka muhimmiyar rawa wajen fito da irin cigaban da matan ke kawo wa a mulkin demokaraɗiyya.

A cewarta matan na kokari sosai wajen gudanar da ayyukan jin kai kuma suna taimakawa wajen kare rayuwar mata, ƙananan yara da matasa.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN