Buhari ya yi wa 'yan Najeriya addu'a a Ka'aba


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shafe lokaci yana yi wa al’ummar kasarsa addu’ar samun zaman lafiya a Masallacin Ka’aba da ke Saudiya, inda ya gudanar da ibadar umarah.

Mai magana da yawun Buhari Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, shugaba Buhari da tawagarsa sun yi wa Najeriya da al’ummarta addu’ar maido da zaman lafiya da tsaro a kasar da sauran kasashen duniya.

Kazalika shugaban ya yi addu’ar farfadowar tattalin arzikin Najeriya wanda annobar Korona ta yi wa illa.

Kazalika Shehu ya ce, shugaba Buhari tare da mataimakin gwamnan Madinah, Yarima Sa’ud Al-Faisal sun shafe tsawon lokaci a cikin Masallacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam, Masallacin da ke zaman a biyu a daraja ga al’ummar Musulmin duniya.

A ranar Litinin da ta gabata ne, shugaba Buhari ya bar birnin Abuja domin halarttar taron zuna jari  karo na biyar da aka gudanar a birnin Riyadh na Saudiya.

RFI Hausa

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN