Dailytrust ta ruwaito cewa aƙalla matasa 172 suka samu taɓin kwakwalwa saboda shan kwayoyi ba kan ƙa'ida ba cikin shekara 6 a jihar Zamfara. Mataimakin kwamandan yaƙi da shan miyagun kwayoyi na hukumar hana sha da fataucin miyaguɓ kwayoyi,
NDLEA, reshen Zamfara, Ladan Hashim, shine ya bayyana haka ranar Alhamis. Mista Ladan, yace hukumar NDLEA reshen jihar Zamfara ta kai matasa da dama asibitin mahaukata domin kula da su.
Ladan ya yi wannan jawabi ne a wurin wani shiri mai taken, 'ÆŠalibai zasu kawo kyakkyawan canji a yaki da shan miyagun kwayoyi a makarantar kwalejin lafiya ta Zamfara.'
Wane nasarori NDLEA ta samu a Zamfara? A cewarsa daga watan Janairu zuwa Satumba, 2021 hukumar ta kama mutane da dama, maza 211 da kuma mata 10 duk masu ta'amali da miyagun kwayoyi. Ya kuma ƙara da cewa a shekarar 2020, hukumar ta samu waɗan da suka saka sami taɓun kwakwalwa 14.
Yace: "Sabida haka masu shan kwayoyi ba bisa ƙa'ida suna bukatar taimakon mu, mu fahimtar da su, kuma mu taimaka musu su samu lafiya ta hanyar ba su kulawa ."
"Da yawan matasan mu suna gidan yari, wasu kuma suna asibitoci neman magani, wasu kuma da yawa sun kamu da manyan cututtuka kamar lalacewar kunhu ko ciwan zuciya da sauransu."
"A wanna yanayin, hanya mafi sauki utace yin amfani da magunguna dai-dai da yadda masan suka yi umarni."
Source: Legit.ng