J
iga-jigan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) a jihar Ondo sun yanke shawarar komawa jam'iyyar PDP, The Nation ta ruwaito.
An cimma matsayarsu ta komawa jam'iyyar PDP ne a wani taro da aka yi a garin Ondo da shugaban jam'iyyar ZLP na kasa Dr. Olusegun Mimiko. Wannan dai shi ne karo na uku da Mimiko zai sauya sheka zuwa PDP.
Sauran shugabannin ZLP da suka halarci taron sun hada da tsohon mataimakin gwamnan Ondo Agboola Ajayi; Hon Gboye Adegbenro da tsohuwar kakakin majalisar Ondo Jumoke Akindele. Hakazalika da shugaban ZLP na Ondo, Hon Joseph Akinlaja; Tsohon dan takarar gwamna Banji Okunomo da kuma tsoffin manyan hadiman Mimiko.
Legit Hausa