Tsufa “cuta” ne da za a iya magancewa


A cewar binciken da aka gudanar sama da shekaru ashirin da suka gabata, ana iya a hana tsufa da wuri, bisa wasu dalilai, don tabbatar da lafiyar mutum na dogon lokaci.

Masanin kimiyya Sinclair ya yi imanin cewa nan ba da jimawa abu ne mai yiyuwa a kawar da tsufa ta hanyar amfani da magunguna, wanɗanda har yanzu ake gwada su kuma "suna iya maganin tsufa."

Masanin kimiyya, likita a Jami'ar Australia, da Cibiyar Fasaha ta Massachusetts a Amurka, yana aiki a dakin gwaje -gwaje na Jami'ar Harvard, inda yake binciken dalilin da ya sa ba ya tsufa.

Ya lashe lambobin yabo da dama a fannin kimiyya. Har ma ya zama sananne.

An zaɓe shi a matsayin ɗaya daga cikin mutum 100 mafi tasiri a duniya, a cewar mujallar Time. Jaridar tana da mabiya kusan 200,000 a Twitter.Tsufa gaskiya ne kuma babu makawa, kuma tsufa ne makomar mutum idan yana raye - amma masanin ilimin halittu David Sinclair ya musanta hakan.

Mai binciken ya kuma kafa cibiyoyin bincike da yawa, wasu daga cikinsu sun mayar da hankali kan tsufa ko hana tsufa.

Haka kuma Sinclair, shi ne marubucin wani littafin 'Lifespan' wato "Tsawon rai" wanda ya yi duba kan abubuwan da kan iya faruwa a kwanakin rayuwa, wanda ya zama littafin da aka fi saya.

Ya yi rubutu game da labarin tsufa da ba makawa, wanda ya yi fice.

Masanin kimiyyar ya yi imanin cewa ya kamata mu canza ra'ayinmu game da shekaru: "Maimakon fahimtarsa a matsayin tsari na al'ada da yanayi na yau da kullum, ya kamata mu ɗauki tsufa a matsayin cuta da za a iya warkarwa," in ji shi.

Sinclair ya ce wannan babban sauyi ne a tunaninmu kan tsufa wanda zai iya taimakawa wajen tsawaita yawancin rai. Kuma don yin watsi da abin da ya kira "tatsuniyar cewa dole ne kowa ya tsufa."

Sauran batutuwan da Sinclair ya lura da su sun haɗa da: "Magani zai iya taimaka mu rayu, idan za mu ɗauki hakan da mahimmanci."

Me ya sa muke tsufa?

Masana kimiyya sun gano abubuwa tara da ke iya haifar da tsufa. Bincikensa na tsawon shekaru 25 da suka gabata ya bayyana biyu kamar haka:

"Ina ganin wadannan sune dalilan da ya sa muke tsufa," in ji Sinclair.

Kun ce ba na son tsufa, don me?

"Babu wani nazarin halittu da ya ce 'dole sai mun tsufa'. Ba mu san yadda za mu kawar da wannan ra'ayin ba amma za mu iya kawar da shi idan muka rage wannan. Kuma ɗakin bincike zai iya yin hakan," in ji shi.

"Yadda muke rayuwa a kowace rana yana da babban tasiri a rayuwarmu ta yau da kullun har ma yana rage kwanakin rayuwarmu."

Yin abubuwan da suka dace na iya rage tsufa.

Bugu da ƙari, sama da kashi 80 na kiwon lafiyarmu a nan gaba ya danganta da yadda muke rayuwa ba bisa ga ƙwayar halitta ba, in ji shi.

Akwai wasu abubuwan da masana kimiyya suka gano ga mutanen da ke da tsawon rai.

Lokacin da kuka kula da nau'in abincin da ya dace da adadin da kuke ci, zai iya taka rawa sosai wajen yaƙar tsufa. Motsa jiki yana taimakawa wajen hana tsufa.

Ta yaya waɗannan abubuwan za su taimaka ga rage tsarin tsufa?

Masana kimiyya sun yi imanin cewa wasu fannoni na rayuwa na iya taimakawa jiki yaƙi da "tsufa".

Masu bincike sun yi imanin cewa motsa jiki, idan aka yi shi da kyau, da cin abincin da ya dace, zai taimaka wajen rage tsufa.

Tsufa na haifar da cututtuka da dama kamar ciwon zuciya da ciwon suga da sauran cututtuka.

Don haka tunanin mayar da mutum ya koma matashi, zai sa ya kasance cikin koshin lafiya.

Wani binciken da aka wallafa kwanan nan a wata mujallar kimiyar hilattar ɗan Adam, ya fito da batun wayewar shekarun baya.

Wannan yana nuna cewa saboda aikin da muke yi, ba za mu iya jinkirta tsufa ko hana mutane tsufa ba.

Shekaru 200 da suka gabata, mutum zai hawa kuma ya yi gudu saman doki.

Akwai dabaru da za mu iya amfani da su don magance wannan matsalar da inganta rayuwa.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN