Yan sakai sun hallaka limamin masallaci da wasu mutum 10 a jihar Sokoto


Wasu yan bindiga da ake tsammanin yan ƙungiyar sakai ne da aka haramta, sun hallaka mutum 11 a Sokoto, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai limamin masallaci daga cikin mutanen da maharan suka kashe a ƙauyen Mamande, ƙaramar hukumae Gwadabawa.

Legit.ng Hausa ta gano cewa baki É—aya mutanen sun mutu ne nan take, yayin da wasu mutum huÉ—u da suka jikkata aka kaisu asibiti domin duba lafiya.
Wane limami aka kashe?
Limamin da lamarin ya shafa, Malam Aliyu, an tabbatar da cewa shine yake jagorantar musulmai sallah a masallacin Salame.

Harin na yan sakai waɗanda aka fi sani da yan bijilanti a Sokoto, ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

Rahoto ya nuna cewa baki É—aya mutanen da aka kashe sun fito ne daga rugar fulani kala daban-daban, inda suka zo kasuwa siyan kayan abinci.

Yan sakai sun farmaki kasuwar ba zato babu tsammani, kuma suka sheƙe mutanen, waɗanda suke zargi da tallafawa yan bindiga.

Shin dagaske mutumin yana jagorantar sallah?
ÆŠaya daga cikin yan uwan limamin, Abdullahi Riskuwa, yace an kashe É—an uwansa ba tare da wata hujja ba domin bashi da wani kashin kaji a jikinsa.

Riskuwa yace:

"Yana da ilimin addinin musulunci kuma ya kasance yana limancin sallah a É—aya daga cikin masallatan mu na garin Salame."

Laifinsa É—aya ne, saboda ya kasance É—an kabilar fulani ne. Amma ba abinda yakai Aliyu kasuwa sai don ya sayi kayayyaki."
Wane mataki jami'an tsaro suka É—auka?
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, yace ba shi da masaniya kan lamarin.

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya haramta ayyukan yan sakai a faÉ—in jihar, kamar yadda Punch ta ruwaito

Legit Nigerian

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN