Kungiyar yan banga na jihar Bayelsa watau Bayelsa State Vigilante Service (BSVS) ta bukaci a yi rijistar masu sana'ar gongo a fadin jihar bayan ta kama wani matashi mai suna Matthew Izibefiezem dan shekara 18 da ya kware wajen satar wayar lantarki da baturarn motoci kuma yake sayerwa yan gongo a babban birnin jihar Yenagoa. Shafin isyaku.com ya samo.
Shugaban kungiyar banga na jihar BSVS, Hon. Doubiye Alagba, ya ce bayan barayin sun saci wayoyin copper da baturan mota sukan sayar wa dilolin sana'ar gongo ciki har da wani fitaccen dila dan arewa mai suna Mr. Bubarak Abdulahi, dan asalin jihar Kano.
Hon Alagba ya ce Allah ya tona asirinsu ne bayan rigima ta kaure tsakaninsu saboda gardama wajen rabon kudiin kayan sata,, lamari da ya jawo jami'an kungiyar banga, kuma suka kamasu ranar Asabar 9 ga watan Oktoba bayan sun saurari bahasi daga barayin.