Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Kasa (NUPENG) ta ce Direbobin Tankar Man Fetur (PTD) za su fara yajin aiki a ranar Litinin kan mummunan yanayin manyan hanyoyin kasar da sauran batutuwa.
Tayo Aboyeji, Shugaban shiyyar kudu maso yamma ta NUPENG, a cikin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Legas ya ce kungiyar ta yi asarar rayuka da dukiyoyi da yawa saboda mummunan hanyoyin.
Leadership Hausa