Sun sace yaro sun karbi N50.000 daga iyayensa kuma asiri ya tonu, duba abin da ya faru da su a bainar jama'a


An kama wasu matasa guda uku aka yi masu dan karen duka a jihar Bayelsa bayan sun sace wani karamin yaro.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa wadanda aka kama masu suna, Miracle a.k.a Mimi, dan asalin garin Wari-Owei da Emi Nokuba mambabin wani gungun mutum shida ne da suka hada baki wajen satar yaron a unguwar Agudama-Epie da ke Yenagoa ranar Juma'a 8 ga watan Oktoba da rana.

Shugaban al'ummar unguwar mai suna Izibeyame Prudent ya sanar da lamarin. Ya ce batagarin sun karbi N50.000 daga iyayen yaron kafin su sako shi. Ya ce sun mika wadanda aka kama ga yansanda.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN